Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: An tara $8bn domin samar da riga-kafin cutar
Hukumar Gudanarwa ta Tarayyar Turai ta yi alkawarin ba da dala biliyan daya domin samar da rigakafin cutar korona.
Hukumar ta yi wannan alkawarin ne yayin wani taron koli domin samar da kudaden gudanar da wani bincike don gano riga-kafin korona,
Shugabar Hukumar Ursula von der Leyen - wadda ita ce mai masaukin baki, ta ce gudanar da bincike domin gano riga-kafin cutar na dukkan kasashen duniya ne.
Cikin shugabannin da suka yi jawabi a taron har da Firai ministan Birtaniya Boris Johnson - wanda ya gabatar da nasa jawabin ta bidiyo daga Landan.
Ya yi bayani kan abin da ya gano yayin da ya kamu da cutar, kuma ya nemi kasasshe da hukumomi da su hada kai domin samar da rigakafin cutar covid-19.
Ya ce tilas "mu dauki matakan da ba a taba dauka ba a kasashenmu, kamar neman 'yan kasashen namu su amince da takura ga rayuwarsu bayan sun saba da 'yanci da walwala."
Ya kuma ce: "amma a gaskiya babu kasar da za ta iya yin nasara kan wannan annobar ita kadai. Idan muna son mu yi nasara, tilas mu hada kawunanmu wuri guda domin samar da rigakafin mai matukar yawa domin amfanin kowa."
Wannan ne karo na farko da aka yi irin wannan taron mai muhimmanci ta hanyar amfani da fasahar zamani - wato intanet a madadin yadda aka saba taruwa a zaure guda.
Fiye da kasashe talatin ne suka halarci wannan taron, cikinsu har da Amurka da China.
An kuma yi alkawarin tara fiye da dala biliyan takwas domin samar da rigakafin cutar korona da ayyukan binciken hanyoyin kulawa da maganin cutar ga wadanda suka riga suka kamu da ita.