Coronavirus: Annobar ta ninka fiye da sau 2 cikin mako a arewacin Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Alkaluman hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya sun nuna cewa a cikin mako guda yawan masu cutar korona ya tashi daga mutum 410 ranar Litinin 27 ga watan Afrilu zuwa 1,301 ranar Litinin 4 ga watan Mayu a arewacin Najeriya.

Adadin ya nuna cewar annobar ta ninka fiye da sau biyu cikin kwana bakwai a tsakanin jiha 18 da kuma birnin tarayya Abuja, inda ta fara bulla a yankin na arewa.

Kano, wadda ta fi fama da yawan masu annobar a arewa, adadin masu cutar ya ninka sau kusan hudu a dan wannan lokaci.

Alkaluman NCDC sun nuna cewa mutum 77 aka gano suna da cutar ranar Litinin ta karshen watan Afrilu, sai dai adadin ya ninninka zuwa 365 bayan mako guda.

Tuni dai, gwamnatin tarayya ta aika wani ayarin likitoci don ya je ya taimaka wajen shawo kan yaduwar korona da kuma mace-macen da aka samu fiye da kima baya-bayan nan a cikin jihar.

A ranar Litinin 4 ga watan Mayu, mutum 147 ne aka tabbatar sun sake kamuwa da cutar a cikin jiha goma da ke yanki, har da birnin Abuja.

Yawan masu cutar a jihohi makwabtan Kano irinsu Katsina da Jigawa ya hauhawa,in ji kididdigar NCDC, don kuwa a Katsina mutum 37 sun sake kamuwa da cutar ranar Litinin, duka-duka tana da masu korona 83.

Sai kuma, jihar Jigawa inda aka samu karin mutum 32 da suka kamu tashi daya, abin da ya sa masu cutar suka kai mutum 39.

Annobar ta fara bulla ne cikin yankin arewa ranar Juma'a 20 ga watan Maris a Abuja, lokacin da Mohammed Atiku ya kamu bayan dawowa daga wata tafiya zuwa kasashen waje.

Ranar Talata 24 ga watan Maris ne kuma aka bayyana bullar cutar cikin jihar farko a arewa, baya ga babban birnin Abuja, inda Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya kamu.

Zuwa yanzu jihar Kogi ce kadai ba a samu bullar wannan cuta ba a daukacin yankin.

Haka zalika a yankin ne annobar ta fara yin kisa a hukumance bayan hukumar dakile cutuka a ranar Litinin 23 ga Maris ta bayyana samun mutum na farko da cutar ta zama ajalinsa.

iyalan Sulaiman A-Ci-Mugu sun ce ya rasu ne tun ranar Lahadi kafin sanar da batun ga jama'a washe gari.

Malam Abba Kyari kuma shi ne mutum mafi girman mukami a Najeriya da cutar ta halaka bayan shi ma an bayyana kamuwarsa a Abuja. Ya rasu ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu.

Kwararru a fannin lafiya na kasar sun ce tuni wannan annoba ta fara fantsama a tsakanin al'umma kuma jihohin arewacin kasar na daga cikin wuraren da har yanzu ake fama da jama'a kan matakan yaki da annobar.

A baya-bayan nan, gwamnatin Kaduna ta ce an gano almajirai fiye da 60 ne da Kano ta mayar mata dauke da cutar korona.

Duk da haka wasu na alakanta karuwar wadannan alkaluma da bunkasar gwaje-gwajen da ake samu, sakamakon karuwar dakunan gwajin cutar korona a yanki.