Messi ya wulakanta ni a gasar Zakarun Turai - Ferdinand

An wallafa

Tsohon dan wasan Manchester United, Rio Ferdinand ya ce ya ji kunyar kansa a wasan karshe da United ta sha kashi a hannun Barcelona a shekara ta 2011.

Dan kwallon Argentina din ya zura wata kwallo mai ban sha'awa da ta bambamce tsakanin kungiyoyin biyu.

Ferdinand ya shaidawa mujallar kwallon kafa ta Copa90 cewa "Messi shi ne bambamcin".

"Messi kamar matsafi ne tare da Ronaldinho, suna yadda suke so da kwallon kafa".

A cewar Ferdinand Barcelona ta koya musu darasi a wasan da aka buga a filin Wembley a 2011.