Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Buhari ya sake bai wa matacce mukamin gwamnati
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya bai wa wani marigayi mukami a gwamnati.
Buhari ya nada marigayi Tobias Chukwuemeka Okwuru a matsayin mamban kwamitin wata ma'aikata watanni biyu bayan mutumin ya rasu.
Sunan Mista Okwuru na kunshe a wata takarda da Shugaba Buhari ya aike wa Majalisar Dattawan kasar ranar Talata ta neman amincewarsu da jerin mutum 37 da ya bai wa mukaman, a watan Fabrairu.
Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan yada labarai, Lauretta Onochie, ta ce Mista Okwuru yana raye lokacin da shugaba Buhari ya nada shi "har ya zo ya gyara takardarsa ta neman daukar aiki".
"Mutumin ya rasu ne a dai-dai lokacin da yake jiran sanatoci su tantance shi kuma ba a sanar da gwamnatin tarayya ba."
Wannan dai ba shi ne karon farko da gwamnatin Shugaba Buhari take yin irin wannan nade-naden matattu mukamai ba.
Ko a 2017 sai da shugaban ya nada mutum biyar da suka dade da mutuwa a matsayin mambobin kwamitocin ma'aikatun gwamnati.