Coronavirus: Dokokin komawa aiki na gwamnatin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatan gwamnatin tarayya a Najeriya za su koma bakin aikinsu daga ranar Litinin 4 ga watan Mayu kamar yadda wata sanarwa daga ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayyar kasar ta fada.
Takardar, wadda shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayyar kasar ya sanya wa hannu, ta ce za a rika bude ofisoshi a ranakun Litinin da Laraba da kuma Juma'a.
Hakan na zuwa ne bayan sassauta dokar kulle ta mako biyar da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya don kare yaduwar cutar korona a biranen Abuja da Legas da kuma Ogun.
Ma'aikata daga mataki na 14 zuwa sama ne aka umurta da su koma bakin aikin nasu inda za su rika tashi da karfe biyu na rana.
An kuma shawarce su da su tabbatar cewa suna bin matakan kariya daga cutar korona kamar yin nesa-nesa da juna da yawan wanke hannayensu a ko da yaushe, da shafa man kashe kwayoyin cuta a hannu da kuma rufe fuska da takunkumi.
Sanarwar ta ce an yi feshin magani a sakatariyar gwamnatin tarayya, kuma za a yi a sauran ma'aikatu da ofisoshi, kazalika an umarci ma'aikatun da su rage yawan masu ziyara.
Legas da Abuja dai sun shafe makwanni biyar a kulle, sannan Legas ce kan gaba wajen masu yawan cutar korona a Najeriya, inda Abuja ke bin ta a baya.







