Coronavirus: 'Ƴan sanda sun kama mutum 65 a otal a Lagos

'Yan sanda

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Rundunar 'ƴan sanda a Jihar Legas ta kama mutum 65 tare da manajan wani otel bisa zargin karya dokar hana fita a birnin.

Ana zarginsu da sharholiya a otel ɗin da sunan halartar bikin zagayowar ranar haihuwar abokinsu.

Gwamnatin tarayya ta sa dokar hana taruka ne a jihohin Legas da Ogun da kuma Abuja, babban birnin ƙasar a yunƙurin karya lagon cutar korona a yankunan.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Jihar Legas ta tabbatar da samun mutum 947 da suka harbu da cutar korona - 20 sun mutu sannan 187 sun warke.

DSP Bala Elkanah, shi ne kakakin rundunar 'yan sanda a Jihar Legas, ya kuma ce tuni suka garƙame otel ɗin.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

Mutanen waɗanda shekarunsu suka kama tsakanin 16 zuwa 45, an kama su ne a otel mai suna Park Hotel a lokacin da suke rakashewa da sunan taya wani daga cikinsu bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

Kazalika jami'an tsaron sun samu wasu daga cikinsu na kwankwadar kayan maye.

"Mun kama su suna shan wasu kayan maye da wasu abubuwa na aikata laifi," a cewar DSP Bala Elkanah. "Wannan ya nuna sharholiya kawai suka je yi."

Ya ci gaba da cewa: "Mun kama wasu da ke rawa babu kaya a jikinsu. Ka san Legas gari ne da aka saba da hutu, yanzu kuma an yi kusan mako huɗu an hana su fita don shakatawa."

'Yan sanda sun ce za a gurfanar da su gaban kotu bisa zargin kin bin umarnin gwamnatin tarayya ta dokar hana fita.