Coronavirus: China na kokarin kayar da ni a zaben Nuwamba - Trump

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce kasar China "za ta yi duk mai yiwuwa" wajen ganin bai sake cin zabe ba a karo na biyu ba.
Mista Trump ya fadi haka ne yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Reuters a Fadar White House, inda ya ce China na fuskantar wasu abubuwa daga Amurka sakamakon barkewar cutar korona.
Donald Trump ya ce China na kokarin ganin abokin hamayyarsa na jam'iyyar Dimokrat, Joe Biden ya buge shi a zaben watan Nuwamba.
Mista Trump ya kara da cewa yana shakkar alkaluman da ke nuna Mista Biden zai lashe zaben watan na Nuwamba.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen China ya yi watsi da zarge-zargen.
Geng Shuang ya ce China na ganin zaben Amurka magana ce ta cikin gida, ya kuma ce yana fatan 'yan siyasar Amurka za su daina amfani da China a harkokin siyasarsu ta cikin gida.
Coronavirus ta yi wa tattalin arzikin Amurka rugu-rugu wanda a baya da shi Trump yake tutiya wajen yakin neman zabensa da za a sake a watan Nuwamba.
Mr Trump, ya kaddamar da yakin kasuwanci da China, amma bai bayyana takamaiman abin da zai yi wa kasar ba.
Sai dai shi kansa Mr Trump ana yawan zarginsa da rashin tabuka komai don kawo karshen matsalar.
Ya shaida wa Reuters cewa: "Akwai abubuwa da yawa da zan iya. Muna duba abin da ya faru.''
Mr Trump ya kara da cewa: "China za ta yi duk abin da za ta iya don sa wa na fadi zaben.''
"Ban yarda da zabukan ba," in ji shugaban kasar. "Na yarda cewa mutanen kasar nan na da basira. Kuma ba na jin cewa za su zabi mutumin da bai cancanta ba.''
'Joe Biden ba zai kayar da ni ba,'' kamar yadda Mr Trump ya sha nanatawa, a yayin tattaunawa da jami'an yakin neman zabensa.
Shugaban Amurka ya sha hantarar manajan da ke jan ragamar yakin neman zabensa Brad Parscale, wanda wanda yake shiga taron ta intanet daga Florida.
Akwai lokacin da ta kai ya zagi Mr Parscale ya kuma ce zai yi kararsa, kamar yadda CNN da Washington Post suka ruwaito, duk da cewa babu tabbas kan ko da gaske yake kan barazanar tasa ta kai shi kara.

Zafafa cacar baka
Sharhi daga Wakilin BBC ta Arewacin Amurka David Willis
Sukar da Shugaba Trump ke yi wa China na karuwa a makwannin baya-bayan nan. Ya kalubalanci adadin wadanda suka mutu tare da cewa yana duba don gano batun da ake yi cewa an kirkiri cutar ne a wani dakin gwaje-gwaje a Wuhan.
Sannan ya ce ya kamata China ta kyale duniya ta san hakikanin abin da ke faruwa dangane da wannan cuta mai yaduwa. Amma wannan ita ce suka mafi tsauri.
Ikirarin da yake cewa China ba ta sanar da duniya batun yaduwar cutar da wuri ba da cewa an kirkiri cutar ne saboda buri na siyasa - da kuma kokarin karawa abokin hamayyarsa Joe Biden karfin cin zabe - Mista Trump yana zafafa cacar baka ne tsakaninsa da kasar.











