An kusa bude Masallatan Haramin Makkah da Madina - Sudais

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban Masallatan Harami guda biyu masu daraja a Saudiyya Shaikh Abdurrahman Sudais, ya ce lokaci ya kusan zuwa da za a dawo yin ibadah a masallatan biyu da ke Makkah da Madina.

Hakan ya bayyana ne a wata sanarwa da shafin Masallatan na Facebook Haramain Sharifain ya wallafa a ranar Talata.

Wani bidiyo ke yawo a kafofin sadarwa na intanet. Sheikh Al-Sudais ya ce: "lokaci na zuwa da fargaba za ta gushe daga al'ummar musulmi kuma za mu dawo masallacin harami domin dawafi da safa da marwa da kuma yin ibadah a masallacin Annabi SAW."

"Abubuwa za su dawo, da izinin Allah kamar yadda suke," in ji Sudais.

Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito ma'aikatar kula da ayyukan Hajji da Umrah na cewa "da yardar Allah karkashin jagorancin gwamnatinmu, da kuma kiyaye umurnin hukumomi, abubuwa za su dawo daidai a Makkah da kuma kai ziyara Masallacin Annabi a Madina daga Musulmi a sassan duniya.

Tun da farko, Sheikh Al-Sudais ya jagoranci dasa kamarori a Masallacin Harami da za su gano wanda ke dauke da cutar korona.

Kamarorin za su iya gano yanayin zafin jikin mutane kusan 25 a lokaci guda, an dasa su a kofar shiga Masallatan Harami a Makkah da Madina.

Duk wannan karfafa guiwar, amma babu tabbas ko za a gudanar da gudanar da Aikin Hajji a bana, yayin da gwamnatin Saudiyya ta nemi kasashen duniya su dakatar da karbar kudaden jama'a domin zuwa aikin Hajji, a yayin da annobar coronavirus ke ci gaba da mamaye duniya.

Tuni hukumomin Saudiyya suka hana shiga Makkah da Madina, da ma Riyadh babban birnin kasar, a kokarin da hukumomin kasar ke yi na hana yaduwar Covid-19.

Hukumomin lafiya a Saudiyya sun ce zuwa yanzu mutum 1,325 suka kamu da cutar korona a kasar, kuma kashi 85 daga cikinsu 'yan kasashen waje ne.