Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Shin ana iya kama cutar daga matacce?
A sassan duniya, cutar korona ta jefa mu cikin wani irin yanayi na kasancewa tare da gawawwaki kuma babu 'yan uwa da za su yi zaman makoki.
Waɗannan al'amura ne da ke kara haifar da fargaba, ba wai kawai mutuwa ita kanta ba, a'a har ma da wadanda ke kwanta dama.
Tsoron yaɗuwar cutar lokacin tabbatar da mutuwar maras lafiya da kuma yiwuwar kamuwa da ɗaukar cutar daga wani wanda ta riga ta kashe.
Shin mamaci na iya yaɗa cutar korona? Ko jana'iza na tattare da hatsari? Ya kamata a binne waɗanda cutar ta kashe? Tambayoyi ne da ke bijirowa a zukatanmu
Ga abin da muka sani.
Shin mamaci na iya yada cutar korona?
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), matukar an bi matakan da suka dace, babu wani dalilin fargaba ko za a iya kamuwa da cutar korona daga jikin wanda annobar ta kashe
Cutar na yaɗuwa ne yawanci daga wani danshi ko ruwa-ruwa da mutum ya fitar, misali lokacin magana ko atishawa ko tari.
Cutar na iya daukar kwanaki a wurin da aka yaɗa ta.
"Zuwa yanzu, babu wata hujja da ke tabbatar da cewa za a iya kamuwa da cutar korona daga jikin wanda ta riga ta kashe, a cewar William Adu-Krow, mai magana da yawun hukumar lafiya ta duniya reshen nahiyar Amurka.
Shin gawar mamaci na dauke da cutar korona?
"Bayan haka, wannan ba ya nufin cewa saboda mun ce cutar ba ta yaduwa daga jikin mamaci, don kana matukar kaunarsa ka je kana sumbatarsa ba, ko wani abu makamancin haka," a cewar masana.
"Ya kamata mu rika kiyaye matakan kariya da kuma matakai."
Shawarwarin hukumar lafiya ta duniya WHO a watan Maris sun bayyana cewa sai dai a yanayi na tsananin zazzabi (kamar Ebola da Marburg) da cutar kwalara, amma gawa ba ta yaɗa cuta.
"Huhun maras lafiya wanda ya kamu da annobar mura, idan aka yi sakaci ba a kula da kyau ba lokacin binciken gawa, ana iya kamuwa da cuta. Idan ba haka ba gawa ba ta yaɗa cuta.
Amma gawawwakin mutanen da suka mutu daga cutukan da suka shafi numfashi na iya kasancewa a jikin mamaci musamman huhu da kuma sauran sassan jiki.
Wadannan za su iya fita a lokacin binciken gawa, inda ake amfani da kayayyakin likita ko kuma wajen yi wa gawa wanka.
'Yan uwa da abokan wanda cutar korona ta kashe ya kamata su tabbatar da an shirya gawar kafin jana'iza ko kuma a bar kwararru su binne ta, musamman masu binne gawa.
Shin za a iya yin jana'iza?
A wasu wuraren, yawan adadin mace-mace masu alaka da korona sun haifar da sabani tsakanin masu binne gawa.
Saboda bin shawarwarin yin nesa-nesa da juna, a kasashe da dama an haramta yin jana'iza. A wasu kasashen kuma ana yi amma an takaita yawan mutanen da za su halarci jana'izar.
Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ta ce 'yan uwa da makusantan mamaci za su iya ganin gawar lokacin jana'iza, idan har sun bi matakan da suka dace.
"Kada su taba ko su sumbaci gawar, kuma su wanke hannayensu sosai da sabulu da ruwa bayan ganin gawar. kuma a kiyaye bayar da tazara (akalla mita daya tsakanin mutane," kamar yadda aka bayyana a shawarwarin WHO.
Bai kamata mutanen da ke fama da mura su je wurin jana'iza ba ko kuma ba tare da sun sanya takunkumi a fuska domin dakile yaduwar cuta.
Kuma kada yara, da manya da suka haura shekara 60 su taba gawar.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce ana iya binne gawa ko kone ta.
"Ba sabon abu ba ne cewa wanda cuta ta kashe a kone shi, amma wannan ba karya ba ne. Kone gawa zabi ne na wasu al'adu."
Wadanda aka dora wa alhakin kula da gawa - misali, wadanda za su saka gawar a kabari, ya kamata su sanya safar hannu kuma su wanke hannu sosai, sannan a dauke kayan da aka yi amfani da su.
Ya zama wajibi kuma a kone ko wanke kayayyakin wanda cutar korona ta kashe, amma a saka safar hannu, idan kuma za a wanke a yi amfani da sabulu mai dauke da kashi 70 na sinadarin ethanol.
Kare martaba
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kamata ya yi a "martabar mamaci da al'adarsa da addini da iyalinsa".
Amma yayin da fargaba ke karuwa, hakan abu ne na da wahalar samu a wasu sassan duniya.
Merwin Terán, shugaban kungiyar masu binne mamata a Ecuador, ya shaida wa BBC Mundo cewa yanayin "ya wuce tunani" a lardin guayas, inda cutar korona ta kashe sama da mutum 10,000 cikin makwanni.
Ecuador ita ce kasa ta biyu a yankin Latin Amurka da suka fi fama da cutar bayan Brazil. Tsarin kiwon lafiya ya gaza shanye matsin lamba; an bar gawawwaki tsawon kwanaki yashe a kan titi yayin da makabartu suka cika.
Asibitoci na tura gawawwaki wuraren ajiye kaya ba tare da yin tanadin da ya dace na adana kaya ko abin sanyaya daki ba.
"Ko mu da muka saba ganin mutuwa a zahiri, yana da wahala mu iya zuwa mu tantance gawa," in ji Terán.
A wasu wuraren hotunan maka-maka kaburbura a New York, da birnin Manaus na Brazil da Santanbul sun mamaye kanun labarai.
Amma gaskiya mai daci a wannan lokaci na cutar korona bai kamata a ce sai an yi bankwana da gawa yadda aka saba ba, a cewar hukumar lafiya ta duniya - amma a ba 'yan uwa damar yin jimami.
"Hukumomi ya kamata su dauki nauyin ko wane yanayi daya bayan daya, tare da mutunta 'yancin 'yan uwa, da bukatar gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar, da hatsarin da ke tattare da kusantar mamaci," in ji hukumar.