Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Za a bai wa iyalan ma'aikatan da suka mutu £60,000
Za a biya iyalan ma'aikatan lafiya da ma'aikatan walwala a Ingila da suka mutu saboda korona fam 60,000, in ji gwamnati
Sakataren Lafiya Matt Hancock ya tabbatar da mutuwar ma'aikatan lafiya 82 da na walwala 16 da suka mutu yayin wannan annobar.
Ya ce yana daga cikin wajibcin aikinsa ''kula da 'yan uwan wadanda suka rasu",
Kungiyar ma'aikatan lafiyar ta yi maraba da wannan sanarwa, tare da yin kira kan a fadada wannan tsarin zuwa wasu ma'aikatun.
Gwamnatin Wales ta yi alkawarin biyan irin wannan kudade ga nata ma'aikatan lafiya da na walwala yayin da Scotland ke yanke shawarar kan yadda za ta yi nata - duk da cewa gwamnatin Burtaniya ke da ikon biyan kudaden.
Sanarwar na zuwa ne kafin a yi shirun jimami na minti daya da karfe 10:00 na safe agogon GMT ranar Talata, don tunawa da ma'aikatan lafiyar da suka rasa ransu yayin yaki da cutar korona.
Firai Minista Boris Johnson shi ma ya yi nasa shirun, tare da wasu mukarraban gwamnati.
Ya sanar da tsarin biyan kudin a bayanin da gwamnatin kasar ke yi kullum, Mista Hancock ya mika ta'aziyyarsa ga ma'aikatan NHS da kuma na walwala.
Ya ce: "Tabbas babu abin da zai maye gurbin wadanda muke so.
Amma za mu iya duk abin da za mu yi domin taimakawa iyalan mutanen wadanda ke fama da wannan rashi."
Babbar sakatariyar kwalejin aikin jinya ta Royal, Donna kinnair, ta ce wannan sabon tsarin biyan kudin zai bai wa iyalan mamatan kwarin gwiwa a wannan halin da suke ciki".
Ta kara da cewa: "Babu adadin kudin da zai maye gurbin mutanen da aka rasa amma kudin da za a ba su zai dan rage musu radadin damuwar da suke ciki.'
'Fadada tsarin'
Shugaban Unison Dave Prentis, shi ma ya nuna farin cikinsa da wannan mataki, yana cewa: "Abin da za mu iya yi ga wadannan mutanen da suka rasa rayukansu dalilin aikinsu shi ne kawai mu ba su wannan kudin domin rage radadi."
Amma kungiyoyin sun nemi da a saukaka wannan tsari a kuma gaggauta shi, a kuma fadada shi zuwa wasu ma'aikatu, kamar wadanda ke aiki a matakin lafiya na farko.
Kungiyar ma'aikata ta yi murna da tsarin amma ta shawarci ministoci da su hanzarta wajen samar da kayan kariya ga mutanen da ke aiki kan gaba wajen yaki da cutar.
'Yar majalisar Jam'iyyar Liberal Democrat Layla Moran, wadda tuntuni ke gangamin wayar da akai game da irin wannan tsarin ta ce, "wannan ne abin da gwarazan ma'aikatan NHS suke bukata kuma suka cancanta".
Ta kuma kara da cewa: "Yanzu akwai bukatar gwamnati ta fadada tsarin ya hada da iyalan duka manyan ma'aikata - masu jinya, malaman makaranta, da direbobin manyan motoci da sauransu - wadanda suka rasa rayukansu a wannan yaki.
"Tsarin ya kamata ya dauki irin wannan mataki kan jami'an soji, a sanya su a tsarin fansho da kuma kudin jana'iza da ake bayarwa."