Coronavirus: Babu ranar dage dokar hana fita a Burtaniya - Boris Johnson

An wallafa

Firai Ministan Birtaniya Boris Johnson a jawabinsa na farko ga jama'ar kasa tun bayan murmurewarsa daga cutar korona ya yi gargadin cewa har yanzu kasar na mataki "mafi hatsari na cutar korona."

Da yake magana a gaban Fadar Downing, Mista Johnson ya ce ba zai yi watsi da sadaukar da kai da mutanen Burtaniya suka yi ba, ta hanyar sassauta dokar hana fita.

"Na san abu ne mai wahala. Ina son bunkasa tattalin arziki cikin sauri ta yadda zan iya. Amma ba zan yi watsi da sadaukarwar da mutanen Birtaniya suka yi ba," in ji shi.

Ya kuma ce yanzu ba za su iya tantance lokacin tabbatar da sauyin ba.

Firai Ministan ya koma bakin aiki ne a ranar Lahadi bayan kwashe makonni uku yana fama da rashin lafiyar cutar korona.

Mista Johnson ya kuma nemi afuwar rashin kasancewa a bakin aikin na tsawon lokacin da bai kamata ba, tare da yi wa abokan aikinsa godiya na rike masa aiki da suka yi - haka nan ya yi wa 'yan kasar godiya saboda bin doka da kuma jajircewa.

'Maharin da ba a gani'

A wani bayani da ya gabatar a safiyar Litinin, Mista Jihnson ya ce ya fihimci damuwar da 'yan kasuwa ke ciki na ganin an kawo karshen wannan doka.

Amma sakin dokar da wuri zai iya dawo da cutar a karo na biyu wanda zai janyo mace-mace da tabarbarewar tattalin arziki da kuma sake kakaba dokar a karo na biyu, in ji Mista Boris.

"Ina rokonku ku kara hakuri," Mista Johnson ya jaddada.

Ya ce "akwai cikakkun alamun da ke nuna cutar na raguwa a Burtaniya" - ciki har da raguwar mutanen da ake kwantarwa saboda cutar korona a sashen kulawa ta musamman a asibiti.

Da yake kwatanta annobar da kamar mutumin da aka kai wa hari, Mista Johson ya ce: "Da a ce wannan cutar wani mahari ne da za ka iya gani kuru-kuru, mahari ne da ba a gani kuma da ba a tsammani - wanda zan iya fada muku daga yadda na ji a jikina, da wannan ne lokacin da ya kamata mu hada hannu mu yake shi mu kai shi kasa.

"Na sani akwai mutane da dama da ke jiran ganin nasarar da aka samu a fili da suka fara mamakin yanzu ne lokacin da ya kamata a sassauta wannan dokar ta nisantar juna."

Mista Johson ya ce Burtaniya ta kare hukumar lafiya ta kasar ya zuwa yanzu, kuma ta fara samun saukin wannan cuta - amma ya ce ba zai iya cewa yaushe ne za a sassuata dokar hana zirga-zirgar ba.

Matukar Burtaniya ta cika sharuda biyar na sassauta dokar, ciki har da raguwar mutuwar da ake samu tare da tabbatar da cewa hukumar lafiya ta kasar za ta iya tafiyar da matsalar ita kadai - "to lokacin ne za mu kara matsawa mataki na biyu" a yakin da muke da wannan annoba, in ji shi.

Amma ya ce: "Yanzu kai tsaye ba za mu iya fitowa mu bayyana sauri ko jinkiri, ko kuma yaushe za a samu wadannan sauye-sauyen ba, amma gwamnati za ta bayyana abubuwa da dama a kai nan da kwanaki masu zuwa."

Ya kuma kara da cewa gwamnati za ta yi kokarin gudanar da komi "a bayyane".

Mai magana da yawun ma'aikatar muhalli Luka Pollar ya ce ya yi matukar maraba da matakin gwamnati na za ta gudanar da abubuwa a bude game da wannan dokar kullen, yana cewa jam'iyyar na bukatar gwamnati ta wallafa duka dabarunta na yaki da cutar.