Coronavirus: Akwai yiyuwar kara tsawaita dokar hana fita a Najeriya

An wallafa

Hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ta nuna cewa lokaci bai yi ba yanzu da za a sassauta dokar hana fita a kasar.

Yayin da kwamitin shugaban kasa kan cutar korona ke bayani kan matakan da ake dauka a ranar juma'a, shugaban hukumar NCDC Dr Chikwe Ihekweazu, ya ce duk da cewa hana fita ya yi mummunan illa ga tattalin arziki amma akwai bukatar a kara hakuri da kara jurewa domin tabbatar da ingantacciyar lafiyar al'umma.

"Za mu wuce wannan lokacin mu koma ga rayuwarmu da muka saba, amma har yanzu ba mu kai ga wannan lokacin ba, don haka nake neman juriya da hakuri da goyon baya."

A ranar Litinin wa'adin dokar hana fita ta tsawon mako biyu da shugaba Buhari ya tsawaita a jihohin Legas da Ogun da kuma babban birnin Tarayya Abuja domin dakile yaduwar cutar korona za ta kawo karshe.

A kallum kuma cutar korona kara yawa take inda ake samun karuwar masu dauke da cutar, da kuma yadda take kara yaduwa a sassan Najeiya.

Zuwa yanzu cutar ta yadu a jihohi 26 na Najeriya hadi da Abuja. Kuma yanzu alkalumman hukumar NCDC sun nuna yawan wadanda suka kamu da cutar sun kai 1,095 yayin da 208 suka warke, 32 kuma suka mutu.

Ana tunanin shugaba Muhammadu Buhari zai kara tsawaita dokar hana fita a jawabin da 'yan kasar suke sa ran zai sake gabatarwa a ranar Litinin.

Akwai yiyuwar kuma dokar da ake tunanin za a tsawaita ta shafi karin wasu jihohi da cutar ta shafa baya ga Abuja da Legas da kuma Ogun, musamman bayan kungiyar gwamnoni ta bukaci shugaban ya kafa dokar hana fita a fadin Najeriya.

Karin labaran da za ku so ku karanta