An ga watan Azumin Ramadana a Saudiyya

Masallacin MAdina

Asalin hoton, Haramain Sharifain

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Kasar Saudiyya ta bayar da sanarwar ganin watan Azumin Ramadana.

Shafin Facebook na Masallatan Harami biyu masu daraja ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa, tare da nuna Sallar Magariba kai-tsaye daga masallacin.

Ganin watan ya sa gobe Juma'a za ta zama 1 ga watan Ramadan na shekarar 1441, wanda ya zo daidai da 24 ga watan Afrilun 2020.

Hukumar Masallatan ta sanar da cewa a ranar Alhamis da daddare ne za a fara gabatar da Sallar Asham, inda Sheikh Shuraim da Sheikh Sudais za su jagorance ta a Masallacin Harami na Makkah, yayin da Sheikh Qasim da Sheikh Budayr za su jagoranci sallar a Masallacin Maznon Allah SAW na Madina.

Sallar Asham a Makkah

Asalin hoton, Haramain Sharifain

Azumi a cikin kulle

Azumin bana dai zai kasance daban da yadda aka saba yin sa sakamakon annobar cutar korona da ta sa aka sanya dokar takaita zirga-zirga a kasashe da dama na duniya don hana yaduwarta.

Dama tuni kasar Saudiyya ta sanya matakan kulle tare da rufe duka masallatan kasar, in ban da haramin Maka da Madina, inda a can din kuma aka takaita mutanen da za su dinga halartar sallar.

Haka Kuma a sanarwar ta ranar Alhamis kasar ta jaddada cewa dokokin za su ci gaba da aiki.

Matakan sun hada da:

  • Masallatan Biyu za su ci gaba da kasancewa a kulle ga jama'a, ma'aikatan hukumar masallatan ne kawai za a dinga bari suna yi sallolin farilla biyar da kuma asham.
  • An rage yawan raka'o'in Sallar Asham daga 20 zuwa 10
  • An dakatar da bayar da abincin buda baki a cikin masallatan
  • Dakatar da Umara da aka yi zai ci gaba kamar yadda aka hana tun farkon barkewar annobar a kasae
  • An soke yin Ittikafi
dokokin masallatan harami

Asalin hoton, Haramain Sharifain