Sabon birnin da zai zama na Indonesiya na fuskantar barazanar Tsunami

    • Marubuci, Daga Jonathan Amos
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Kimiyya
  • An wallafa

Masana kimiyya sun gano barazanar afkuwar girgizar teku na tsunami risk a yankin da Indonesiya ta zaba don zama babban birninta.

Masu bincike sun gano hujjoji da ke nuna cewa ana samun zaftarewar laka da dama a karkashin teku a ruwan Makassar Strait tsakanin tsibiran Borneo da Sulawesi.

Idan irin haka ta sake faruwa a yau, to zai jawo tsunami inda Tekun Balikpapan - wani yanki da ke daf da inda ake son yin sabon babban birnin kasar zai yi ambaliya.

Amma tawagar ta ƙasa da ƙasa ta ja kunne kada a wuce makaɗi da rawa wajen zuzuta lamarin.

''Muna da sauran aiki a gaba na tantance hakikanin halin da ake ciki. Bayan nan, wannan wani abu da ya kamata a ce gwamnatocin Indonesiya sun shigar cikin hadurran da ake fusukanta, ko da kuwa muna maganar sauran abubuwa ne,'' a cewar Dr Uisdean Nicholson na Jami'ar Heriot-Watt ta Burtaniya.

Tawagarsa ta masu bincike daga Birtaniya da Indonesiya ta yi amfani da bayanan motsin ƙasa wajen binciken ƙasar da ke shimfide a ƙarƙashin tekun Makassar.

Binciken ya bayyana cewa laka da turbaya da yashin sun gangara sun kara shiga ruwa.

Wasu daga cikin motsin ƙasar sun rutsa da dubban kilomita na abubuwa waɗanda sun ma fi ƙarfin su jijjiga ruwan kuma su samar da manya-manyan igiyar ruwa a saman tekun.