Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Samaniya ta zama tamkar garwashi a Indonesia
Sararin samaniyyar lardin Jambi na kasar Indonesia ya yi ja ja zur kamar jini a karshen mako sakamakon bazuwar wutar dajin da ta mamaye sassan kasar daban-daban.
Wani mazaunin yankin wanda ya dauki hotunan saman ya ce "bujin na da makaki a makogaro da idanu".
A kowace shekara dai wutar daji na haddasa bujin da yake rufe kusan daukacin kasar.
Wani masanin yanayi ya shaida wa BBC cewa yanayin sararin samaniyyar ya faru ne sakamakon bazuwar abin da ake kira Rayleigh.
Ma'aikata mai kula da yanayi ta kasar BMKG ta ce hotunan tauraron dan adam sun nuna wuraren da abin ya fi kamari a kewayen shiyyar Jambi.
An dai ce hazon irinsa ne mafi muni a tarihin kasar. Duk da cewa a kan samu yanayin bujin daga watan Yuli zuwa Oktoba.