Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Me ya sa ake son yi wa masu cutar korona ruf da ciki?
- Marubuci, Daga Fernanda Paúl *
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
- An wallafa
Yayin da masu kamuwa da cutar korona ke kara yawa a fadin duniya, muna kara sabawa da hotunan asibiti da muke gani yau da gobe.
Amma muna ganin marasa lafiya da ake kai wa sashen kulawa na musamman, da ake sanya wa na'urar taimakawa numfashi don taimaka musu, amma abu guda ciki na jan hankulanmu.
Me yasa da yawa daga cikinsu ke kwanciya kan cikinsu?
Wannan tsohowar hanyar ana kiranta "ruf-da-ciki" an ta nuna yadda ta taimaka wa marasa lafiya da ke fama da matsalar numfashi.
Tana taimakawa karuwar numfashin da ke shiga cikin huhunsu.
Amma wannan dabarar ita ma na da nata hadarin.
Karuwar shigar numfashi
Marasa lafiya ana juya su, su yi kwanciyar ruf-da-ciki na tsawon sa'o'i domin fitar da dattin da ke toshe huhunsu ya kawo tsaiko wajen yin numfashi.
Ana kara ci gaba da wannan dabara wajen lura da masu korona wadanda ke bukatar kulawa ta musamman.
"Mafi yawan wadanda suka kamu da korona ba sa iya samun tara iska a hnhunsu wanda hakan ke cutar da su", in ji Panagis Galiatsatos, wani kwararren likita kuma babban malamin Jami'ar Johns Hopkins da ke Amurka.
"Duk da cewa suna samun taimako karuwar numfashi, amma hakan ba ya isa a lokuta da dama. Abin da muke yi sai mu kifa su fuskarsu kasa su kwanta a kan cikinsu, domin ya bai wa numfashinsu damar budewa sosai.
Dakta Galiatsatos ya ce bangaren da ya fi nauyi a jikin huhu daga baya yake, to idan marasa lafiya na rigingine suna kallon sama hakan ba ya ba su damar shakar iskar da za ta ishe su.
Maimakon hakan, dabarar ruf-da-ciki na kara yawan numfashin da ke shiga sassa daban-daban na huhunsu.
"Hakan zai iya samar da wani sauyi da za mu iya gani take cikin gaggawa, mun ga hakan wajen marasa lafiya da yawa," in ji Dakta Galiatsatos.
A watan Maris, Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ta ba da shawara a rika kifa dattijai masu fama da cutar korona da ke fama da matsalar numfashi a kan cikinsu na sa'o'i 12 zuwa 16 a kullum.
Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ta ce ya kamata a rika amfani da dabarar a kan kananan yara, amma hakan na bukatar karin mutane da suke da kwarewa sosai, don gudanar da ita cikin kwanciyar hankali.
Wani bincike da kungiyar likitotin kashi ta Amurka ta yi, kan marasa lafiya 12 da ke fama da cutar korona da ke bukatar kulawa ta musamman, wadanda aka kwantar a asibitin Jinyintan na Wuhan a watan Febrairu, ya gano cewa marasa lafiyar da ba su dade a ruf-da-ciki ba sun fi fama da matsalar huhun, idon aka kwatanta da wadanda suka yi ruf-da-ciki.
Hadarin dabarar ruf-da-ciki
Duk da cewa kamar da sauki wajen yin kwanciyar, amma ruf-da-ciki na zuwa da matsaloli.
Kifa marasa lafiya kan ruwan cikinsu yana daukar lokaci kuma abu ne da ke bukatar kwarewa da gogewa.
"Ba abu ba ne mai sauki. Ana bukatar mutum hudu zuwa biyar don juya mara lafiya kamar yadda ya kamata," in ji Dakta Galiatsatos.
Hakan ya nuna cewa abu ne mai wuya ga asibitocin da ke da karancin ma'aikata kuma suke fama da karin marasa lafiyar korona da ake kwantarwa.
Asibitin Johns Hopkins ya ware wata tawagar kwararrun da ke aikin kifa mutum, saboda daukar mataki kan karuwar masu fama da korona da ke kara yawa, in ji Dakta Galiatsatos.
"Don haka idon masu korona na sashen kulawa ta musamman inda ma'aikatan wajen ba su saba da wannan kwanciyar ba, sai su garzaya su kira wo kwararru a wajen ruf-da-ciki."
Sauya wa marasa lafiyar kwanciya kan iya haifar da wasu matsalolin na daban.
"Kiba na daya daga cikin matsalolin da muke fuskanta. kuma dole muyi taka tsantsan da mutanen da ke da matsala a kirjinsu, da kuma marasa lafiyar amfani da na'urar taimakawa numfashi."
Wannan dabarar kifa mutanen na da alaka da hadarin kamuwar ciwon zuciya a wasu lokutan za ta iya haifar toshewar hanyoyin iskar jikin dan adam.
Dabarar na kara karbuwa yanzu
An fara amfani da wannan dabarar ne a tsakiyar shekarun 1970.
Amma ba ta karbu ba har sai a 1986 asibitoci suka fara amfani da ita a duniya, kamar yadda kwararru suka ce.
Luciano Gattinoni na daya daga cikin likitocin da suka gudanar da bincike kan wannan dabarar - kuma sun samu nasarar gwada ta kan marasa lafiya da yawa.
Farfesa Gattinoni ya shaida wa BBC dabarar rif-da-cikin ta fuskanci ce-ce-ku-ce lokacin da aka fara amfani da ita, daga kungiyoyin likitoci masu ra'ayin rikau.
"Amma yanzu ko ina ana amfani da ita" in ji Farfesan.
Ya kara da cewa karuwar numfashin da ke shiga huhu ba shi kadai ne alfanun da ake samu daga rif-da-cikin ba.
"Yayin da marasa lafiyan ke kallon kasa, dukkan sauran sassan hunhu na kara budewa," Farfesa Gattinoni.
"Idan ka kalli yadda hunhu ke kara samun karfi daga na'urar taimakawa nunfashi: zai zama yana ci gaba da bugawa. kuma yawan bugawar da yake, na nufin karancin cutuwar da zai iya fuskanta."
An ta samun wallafe-wallafen da ke goyon bayan amfani da wannan dabarar a farkon wannan karnin.
"Wani bincike da aka gudanar a Faransa a 2000, masara lafiyar da aka kifa su ba kawai karuwar nunfashi suke samu ba, suna samun damar ci gaba da rayuwa sosai."
Daga baya, wadaddan duka bayanai ne da ke kalubalantar wannan annoba da ta kashe dubban mutane - da kuma wasu wadanda har yanzu ke fama da ita.