Coronavirus a Kano: Mutum 18 sun mutu, 65 sun sake kamuwa a rana guda

Testing for covid-19

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ma'aikatar lafiya ta jihar Kano a Najeriya ta ce ya zuwa daren Juma'a, an samu karin mutum 65 da suka kamu da cutar sarkewar numfashi ta korona a jihar.

Hakan na nufin adadin mutanen da ke dauke da cutar a Kano ya kai 547, tun bayan bullar cutar a jihar, sai dai kuma an sallami mutum 20, inda 18 suka riga mu gidan gaskiya.

Jadawalin jihohin da cutar ta bulla da hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya, NCDC ta fitar ya nuna Kano ce ta biyu a yawan masu fama da cutar bayan Legas mai mutum 1,667 da Abuja babban birnin kasar inda ake da mutane 336.

A ranar 11 ga watan Afrilu ne hukumomi a Kano suka sanar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar kuma tun daga wannan lokacin aka rika samun karuwar mutanen da annobar ta shafa, kuma ci gaba da gwaje-gwaje a jihar bayan an sami tsaiko ya sa aka samu karuwar yawan wadanda ke dauke da cutar.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Kano

Asalin hoton, Getty Images

Karin bayani kan coronavirus

Alkaluman mutum 65 da hukumar NCDC ta fitar a daren Juma'a na wadanda suka kamu da cutar na nuni da yadda annobar ke kara bazuwa a jihar ta Kano.

A yanzu dai cutar na kara bazuwa a jihohin da ke makwabtaka da Kano - Katsina na da mutum 137 sai Jigawa mai mutum 83, Bauchi na da 117 yayin da Kaduna kuma ta ke da mutum 95.

A cewar sanarwar da hukumar NCDC ta fitar a Twitter, zuwa daren Juma'a, mutum 3,912 ne suka kamu a jihohi 34 har da Abuja. Daga cikin adadin, 679 sun warke har ma an sallame su daga asibiti.

Sai dai adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar ya karu, inda jimilla mutane 117 suka riga mu gidan gaskiya.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2