Goma sun sake kamuwa da coronavirus a Kano

Gwamna Ganduje

Asalin hoton, Twitter/@dawisu

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Adadin mutanen da suka kamu da cutar korona zuwa daren Asabar 18 ga watan Afrilu ya kai 37 a Kano, bayan sanar da karin mutum goma da annobar ta harba.

Kano, mafi yawan jama'a a Najeriya a yanzu ita ce ta uku a yawan wadanda suka kamu da kwayar cutar, baya ga Legas da Abuja, har ma ta yi sanadin mutuwar mutum guda a ranar Laraba.

A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, ma'aikatar lafiyar jihar ta ce ya zuwa karfe 10:51 na daren Asabar, "adadin masu cutar korona a Kano ya kai 37, sannan mutum guda ya mutu."

Wannan adadi na zuwa ne mako guda da bullar annobar karon farko a Jihar.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

A wannan Juma'ar ce ma'aikatar lafiya ta jihar Kano ta sanar cewa shugaban kwamitin yaki da cutar a Kano ya kamu da covid-19.

Ranar Asabar 11 ga watan Afrilu ne, hukumomi suka bayyana samun mutum na farko da ya kamu da annobar a jihar.

Bayanan da hukumomi suka fitar sun nuna cewa mutumin, wanda mazaunin karamar hukumar Tarauni ne, ya baro Abuja inda ya isa Kano a jajiberin ranar da za a rufe hanyoyin shiga jihar.

Gwamnatin Kano ta yi feshin magani a wuribiyar da mutumin ya kai ziyara kafin a gano cewa yana dauke da cutar.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

A hirarsa da BBC kan bullar cutar coronavirus a Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce za a dauki tsauraran matakai domin kare al'ummar jihar.

Daga cikin matakan, Gwamnan ya haramta wa 'A daidaita sahu daukar mutum fiye da daya', ko da yake daga bisani an amince a rka daukar mutum biyu.

Su ma motocin haya, an hana su daukar mutane fiye da kima.

Kazalika, gwamnatin jihar ta ce za ta dauki matakai na rufe wasu kasuwanni, a cewarta za a bar kasuwannin da ke sayar da kayan abinci da sauran kayan tilashin rayuwa su ci gaba da budewa.

Da ma tuni aka samu bullar cutar a jihohin da ke makwabtaka da Kano, wato Kaduna da Katsina.

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa NCDC ta ce ya zuwa daren Asabar ta tabbatar mutum 542 ne suka kamu da cutar, 166 ne kuma suka warke yayin da 19 suka mutu sakamakon korona a fadin kasar.

Karin labarai masu alaka: