Wadanne jihohi coronavirus ta bulla cikinsu a Nigeria?

Asalin hoton, @jidesanwoolu
An samu karin mutum 13 sabbin kamuwa da cutar coronavirus ranar Asabar 11 ga Afrilu a Najeriya, kuma Kano ta zama jihar da a baya-bayan nan cutar ta bulla cikinta.
Gwamnatin Kano ta ce tuni aka kebe dattijon wanda tsohon jami'in gwamnati ne, har ma an debi samfurin jikin iyalinsa, don yi musu gwaji su ma.
Lamarin na zuwa ne duk da matakan da hukumomi ke dauka a kasar ciki har da jihohi kamar Kano, inda gwamnati ta ce ta rufe iyakokinta don hana shiga ko fita, tare da bullo da matakan rage tarukan jama'a.
Kwana hudu ke nan bayan samun mutum na farko da ya kamu da cutar covid-19 a makwabciyar Kano wato jihar Katsina, kafin daga bisani gwajin da aka yi wa iyalin marigayin ya nuna uku daga cikinsu su ma sun kamu.
Kano ce jiha mafi yawan mutane a Najeriya kuma ta uku a shiyyar Arewa maso Yamma da aka samu bullar cutar coronavirus, baya ga Kaduna da Katsina.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa NCDC ta ce zuwa yanzu mutum 318 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a daukacin Najeriya, a cikinsu goma sun rasu. Saba'in kuma sun warke, an sallame su.
A cewar alkaluman hukumar, fiye da rabin masu fama da cutar a Najeriya suna jihar Legas, inda aka tabbatar annobar ta fara bulla ranar Alhamis 27 ga watan Fabrairu.
Wani baturen kasar Italiya ne da ya zo Najeriya daga birnin Milan, kuma bayan saukarsa a filin jirgin saman Legas, ya yi tafiya zuwa jihar Ogun mai makwabtaka.
A yanzu haka dai, hukumar NCDC ta ce akwai mutum 174 da ke jinya sakamakon annobar coronavirus a jihar ta Legas, sai kuma Abuja da ke biye wa Ikkon da masu cutar 56.
Gwamnan Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa a ranar 11 ga watan Afrilu an kara sallamar marasa lafiya hudu da suka warke daga cutar cikinsu har da wani yaro dan shekara 11.
A cewarsa, da wannan, yanzu adadin mutanen da suka warke daga annobar a jihar Legas sun kai 50.

Asalin hoton, @jidesanwoolu
Bauchi, ita ce jihar da aka fara samun mutumin da ya kamu da cutar a tsakanin jihohin arewacin Najeriya, ban da Abuja. Gwajin da aka yi wa Gwamna Bala Mohammed ya nuna cewa ya kamu da cutar ranar 24 ga watan Maris.
Rahotanni sun ce ya yi hulda da mutum na farko da cutar ta shafa a Abuja, babban birnin kasar wato Mohammed Atiku wanda aka yi masa gwajin da ya tabbatar yana dauke da coronavirus ranar 20 ga wata.
Daga bisani dai, gwamnan jihar ta Bauchi, wadda aka tabbatar zuwa yanzu mutum shida ne a jihar suka kamu da annobar, ya warke bayan gwaji na biyu da aka yi masa, inda ya fito daga wurin da aka kebe shi ranar 9 ga watan Afrilu.
Cutar dai ta shiga daukacin jihohin Kudu maso Yamma na Najeriya, kuma baya ga jihar Legas, Osun na da mutum 20 da ke fama da cutar, ko da yake a baya-bayan nan gwamnan jihar Gboyega Oyetola ya tabbatar cewa mutum 10 sun warke.

Asalin hoton, @GovKaduna
Jihar Ekiti na da mutum biyu da ke da cutar, sai Oyo da ke da mutum 11, Ogun jihar da cutar ta fara bulla bayan Legas zuwa yanzu akwai mutum bakwai da ke jinya sanadin annobar.
Kaduna ma mai makwabtaka da Kano ta bangaren arewa da kuma Abuja ta bangaren kudanci, an samu mutum na shida da cutar ta harba ranar Asabar 11 ga Afrilu.
Jami'ai sun ce mutumin namiji ne wanda yake aiki a matsayin mai gadi cikin unguwar Mando kuma a baya-bayan nan ya koma gida daga tafiyar da ya yi zuwa Lagos.
Har yanzu mutumin da ya fara kamuwa da cutar a Kaduna, Gwamna Nasir El-Rufa'i yana ci gaba da jinya bayan gwajinsa ya fito ranar Asabar 29 ga watan Fabrairu.
Neja da Anambra su ne jihohin da cutar ta bulla cikinsu ranar Juma'a 10 ga watan Afrilu, a yanzu haka kowaccensu na da mutum guda da ke fama da cutar.
A yankin Arewa ta tsakiya cikin jihar Kwara, akwai mutum biyu masu cutar, yayin da jihar Binuwai ke da mutum guda.
Jihohin Kudu maso Kudu, Edo ce ta fi yawan masu coronavirus da mutum 12, sai jihar Akwa Ibom mai mutum biyar, Delta na da uku, Rivers kuma biyu.
A yankin Kudu maso gabashin Najeriya, baya ga Anambra, jihar Enugu na da mutum biyu da ke jinya sakamakon annobar.
Ga adadin mutanen da suka kamu da cutar cikin jihohin da annobar ta bulla.
Lagos- 174
FCT- 56
Osun- 20
Edo- 12
Oyo- 11
Ogun- 7
Bauchi- 6
Kaduna- 6
Akwa Ibom- 5
Katsina-4
Delta- 3
Enugu- 2
Ekiti- 2
Rivers-2
Kwara- 2
Ondo- 2
Benue- 1
Niger- 1
Anambra- 1
Kano-1

Asalin hoton, @NCDCgov
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya ta ce an kafa karin dakunan gwaje-gwaje guda biyu, wadanda ke da kayan aikin da za a iya tantance samfurin cutar a jihohin Kano da kuma Filato.
A baya dai an yi ta korafe-korafe kan rashin cibiyar gwada cutar coronavirus ko guda daya a yankin arewacin kasar mafi yawan jama'a.
Yanzu dai hukumar NCDC ta ce akwai cibiyoyin gwaje-gwajen guda 11 a fadin kasar, ko da yake rinjanyensu suna kudu ne.
Hukumar dai ta ce ana ci gaba da ayyuka don ganin an kammala cibiyoyin gwaje-gwajen da ake kafawa a biranen Maiduguri da Sokoto da Fatakwal da kuma Kaduna.









