Adadin mutanen da suka mutu a Najeriya ya kai 10 - NCDC

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar dakile yaduwar cutuka a Najeriya ta ce ya zuwa karfe 9:30 na daren ranar Asabar, an samu karin mutum 13 da suka kamu da coronavirus a kasar.
Wannan na nufin adadin mutanen da suka kamu da cutar a kasar ya kai 318 jimilla.
Hukumar ta ce 11 daga cikin karin mutum 13 na Jihar Legas sai 1 a Delta da kuma daya a Kano - jiha ta baya-bayan nan da cutar ta bulla.
A cewar hukumar, cutar ta covid-19 ta bulla a jihohi 19 cikin 36 da ke kasar kuma kawo yanzu, an sallami mutum 70 daga asibiti sai guda 10 da suka riga mu gidan gaskiya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
- Lagos- 174
- FCT- 56
- Osun- 20
- Edo- 12
- Oyo- 11
- Ogun- 7
- Bauchi- 6
- Kaduna- 6
- Akwa Ibom- 5
- Katsina-4
- Delta- 3
- Enugu- 2
- Ekiti- 2
- Rivers-2
- Kwara- 2
- Ondo- 2
- Benue- 1
- Niger- 1
- Anambra- 1
- Kano-1


Karin labaran da za ku so ku karanta








