Ko akwai yiwuwar kawo karshen coronavirus a Abuja?

An wallafa

Yayin da alkaluman wadanda suka kamu da annobar covid-19 ke karuwa a Najeriya, mazauna biranen da annobar cutar ta bulla na cikin zullumi a kan ko yaushe za a kawo karshen cutar a kasar.

Abuja, shi ne babban birnin tarayyar kasar, kuma na biyu a cikin jerin biranen da suke da masu dauke da wannan cuta, inda adadin masu cutar a birnin ya zuwa yanzu ya kai 54.

Sakamakon yaduwar da wannan cuta ke yi a kasar gwamnati ta sanya dokar hana fita ta tsawon mako biyu a birnin Abujan da jihar Legas da kuma Ogun.

Duk da wannan dokar hana fita a birnin na Abuja, har yanzu ba a daina samun sabbin wadanda ke kamuwa da ita ba.

Wannan dalili ne ya sa mazauna birnin ke tunanin ko yaushe za a kawo karshen wannan cuta a Abujan da ma Najeriyar baki daya?

BBC ta tattauna da Farfesa Abdusalam Nasidi, shugaban kwamitin da zai kula da sa ido da gudanar da asusun ayyukan taimakawa al'umma a wannan lokaci na yaki da coronavirus a Abuja, inda aka tambaye shi - ko yaushe ne ake sa ran cin karfin wannan cuta a babban birnin tarrayar?

Farfesan ya ce " Idan har mutane za su kiyaye da ka'idojin da shugaban kasa ya sanar a jawabin da ya yi wa kasa da kuma amfani da shawarwarin da hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta kasar ta bayar, to ko shakka babu za a kawo karshen wannan cuta.

Shugaban kwamitin ya ce, shawarwari kamar wanke hannaye da barin tazara, barin shiga cunkoso da dai makamantansu, sune abubuwan da ya kamata mutane su kiyaye ba a Abuja ba ma kadai a ko ina.

Ya ce ''idan har aka kiyaye to cutar coronavirus za ta zamo tarihi a Abuja da Najeriya kai har ma da sauran kasashen duniya''.

Farfesa Abdusalam Nasidi, ya ce amma idan har aka ki amfani da shawarwarin sannan mutane kuma suka ci gaba da abin da suka ga dama, to za a fuskanci abin da ba zai wa kowa dadi ba a Abujan da ma Najeriya baki daya.

Daga bisani farfesan ya ja hankalin mazauna Abuja da ma Najeriya, a kan da zarar sun fuskanci basa jin dadi a jikinsu, misali ko suna tari ko zazzabi mai zafi ko ciwon makogoro ko kuma suka fuskanci basa iya numfashi sosai to su yi maza su je asibiti.

Ya ce yin hakan zai matukar taimakawa wajen kawo karshen coronavirus a Abuja dama Najeriya.

Karin bayani

Ya zuwa yanzu dai akwai mutum 288 da ke dauke da wannan cuta, inda 55 suka warke 6 kuma suka mutu.

Tuni dai jihohin Najeriya da dama suka dauki matakan dakile yaduwar wannan cuta ciki har da jihohin da cutar ma bata bulla ba.

Jihar Legas ce dai tafi yawan masu dauke da wannan cuta, sai kuma Abuja babban birnin Najeriyar.