Coronavirus: ‘Yan sandan Najeriya sun kama ‘yar fim saboda ta tara jama’a

An wallafa

'Yan sanda a birnin Lagos da ke Najeriya sun kama fitacciyar 'yar fim din nan Funke Akindele saboda ta hada bikin murnar zagayowar ranar haihuwar mijinta, JJC Skillz, inda aka yi tara jama'a.

Taron da ta hada ya karya dokar hana fita da gwanatin Najeriya ta sanya a jihohin Lagos da Ogun da kuma babban birnin tarayyar kasar, Abuja, a cewar kakakin rundunar 'yan sandan jihar Lagos, Mr Bala Elkana.

Mr Elkana ya bukaci mutanen da suke je gidanta domin taya ta bikin su mika kansu ga rundunar 'yan sanda zuwa ranar Litinin idan ba haka ba a ayyana su a matsayin wadanda ake nema ruwa-a-jallo.

Da ma dai ranar Lahadi masu bibiyar shafukan sada zumunta musamman shafin Twitter a Najeriya, sun caccaki tauraruwar fina-finan kudancin Najeriyar bisa karya dokar hana fitar.

Funke Akindele na cikin wadanda suka dinga wayar da kai a kan coronavirus a cikin wani bidiyo da hukumar NCDC mai yaki da cutuka masu yaduwa ta shirya.

Sai dai tauraruwar ta ce baki dayan mahalarta bikin sun shafe sati biyu a gidan nata kafin shagalin.

Amma fa tuni ta goge sakon na Twitter da ta wallafa.

Cikin wadanda suka halarci bikin har da fitaccen mawakin nan Naira Marley da tauraruwa Eniola Badmus.