Coronavirus a Nigeria: Mun fara ganin yaduwar annobar a tsakanin 'yan kasar - Likitoci

NMA

Asalin hoton, NMA

Bayanan hoto, Kungiyar likitocin Najeriya ta bukaci a fadada kwamitin kar-ta-kwana mai yaki da coronavirus a kasar ta yada zai kunshi 'yan jarida da masu fafutuka
An wallafa

Yayin da annobar coronavirus take ci gaba da barna a Najeriya, dambarwa ta kaure tsakanin kungiyar likitocin kasar da gwamnati, a kan gayyato likitoci daga kasar China don su taimaka wajen yaki da cutar.

Wata sanarwa da kungiyar likitoci a Najeriya ta fitar na cewa cin fuska ne, ba tare da tuntubarsu ba gwamnati ta gayyato takwarorinsu na kasar China.

Suka ce gayyatar "wani abin damuwa ne da matukar ban takaici".

Sanarwar wadda ta wallafa a shafinta na intanet ta ce abin kunya ne ga likitocin Najeriya da sauran ma'aikatan lafiya wadanda suka tsaya iyakar iyawa suna ba da gudunmawa a yakin da kasar ke yi da annobar coronavirus, duk da mummunan yanayin aiki da tsarin kula da lafiya maras inganci amma gwamnati ta zagaye ba tare da tuntube su ba.

Liktocin sun kuma bayyana damuwa a kan rashin rigunan kare jami'an lafiya da karancin kayan gwaje-gwaje da ma cibiyoyin gwaje-gwajen a fadin kasar.

"Kuma matukar rashin duk wani nau'in shirin inshora ga ma'aikatan lafiya tun asali (na daga cikin) batutuwan da ke bukatar a mayar da hankali kansu." in ji sanarwa.

Likitocin sun bayyana gagarumar damuwa cewa gwamnati ba ta yi la'akari da dokokin da ke kula da aikin likitanci a kasar ba.

Suka ce maimakon kwaso baki da ake da damuwa game da batun tsaron kasa a kansu kuma ba su san al'ada da yanayi da kalubalan da suka kebanta da Nijeriya ba, kungiyar ta kwan da sanin dumbin ma'aikatan lafiya da kwararru a wannan bangare wadanda ko dai ba su da aikin yi ko kuma aikinsu ya gaza kwarewarsu, wadanda kuma suna iya taimaka wa a wannan al'amari.

Kungiyar ta ce kamata ya yi gwamnati ta nuna godiya ga ayyukan likitoci da ma'aikatan lafiyan da ke aiki da cibiyar dakile cutuka masu yaduwa da cibiyoyin kebe masu coronavirus wajen zuba dukiya da gudunmawar da aka samu don inganta dakunan gwaje-gwaje da nufin gano karin mutanen da suka kamu da cutar.

Da take watsi da gayyatar da ta ce gwamnati ta yi wa likitocin kasar China, kungiyar ta ce maimakon haka tana kira ga gwamnati ta yi bitar tsarin kyautata jin dadin likitoci da ke bakin fama.

Ta ce matakin farko da ya kamata gwamnati ta bi shi ne samar da wadatattun rigunan kare jami'an lafiya da bude karin cibiyoyin kebe marasa lafiya tare da zuba kayan aiki da suka dace a fadin kasar.

Likitocin sun ce ya kamata a samar da karin kayan aiki don saukaka gwaje-gwaje don kuwa "mun fara ganin yaduwar cutar covid-19 a tsakanin al'ummar kasa.

Ba a gurbata kayan aiki da coronavirus ba

A wani al'amarin kuma, Cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta Nijeriya ta yi watsi da zarge-zargen cewa wasu kayan aikin likitanci da aka kawo daga kasar China an gurbata su da cutar koronabairas.

A wani sakon Tiwita da ta wallafa a intanet, cibiyar ta ce babu wata shaida da ke nuna irin wadannan kaya sun gurbata da cutar covid-19, don haka kayayyakin suna da inganci matukar ma'aikatan lafiya sun yi amfani da su cikin aminci.

A makon jiya ma sai da ministan labaran Najeriya shi ma ya yi watsi da ikirarin cewa kayan aikin da biloniyan kasar China Jack Ma da gwamnatin kasar suka bai wa Najeriya gudunmawa ba su da inganci.

Masu koronabairas sun karu

Cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya ta tabbatar da samun karin mutum 18 da ya kamu da cutar da coronavirus ranar Lahadi a kasar.

Ta ce an kuma sallami marasa lafiya 33 da suka warke daga wannan cuta zuwa yanzu.

Adadin masu covid-19 a jihar Legas kadai ya kai 120, Abuja kuma na da mutum 47 da ke fama da sarkewar numfashin. A Kaduna an samu karin mutum guda inda adadin masu cutar ya kai biyar a yanzu.

A cewar cibiyar tun bayan barkewar cutar ranar 27 ga watan Fabrairu zuwa yanzu mutum biyar ne coronavirus ta yi ajalinsu a Najeriya.