Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan bindiga 'sun kashe mutum 22 a Sokoto'
Rundunar 'yan sandan Sokoto da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da cewa 'yan bindiga sun kashe akalla mutum 22 ranar Laraba a harin da suka kai a wani kauye da ke jihar.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Mohammed Abubakar Sadiq, wanda ya shaida wa BBC wannan labari, ya kara da cewa 'yan bindiga, wadanda suka kai harin a kauyen Gangara da ke karamar hukumar Sabon Birni, sun kuma jikkata mutane da dama.
Ya kara da cewa 'yan bindigar sun yi kokarin yi wa dakarun soji da jami'an 'yan sandan da suka je kauyen domin fafarar su kwanton-bauna, amma basu yi nasara ba kuma an kashe dan bindiga daya.
Ya kara da cewa kwamishinan 'yan sandan jihar, Ibrahim Sani Ka'oje, ya bayar da umarni a gudanar da bincike domin gano ainihin abin da ya faru a kauyen yana mai cewa nan gaba kadan za su yi karin bayani kan lamarin.
Jihar ta Sokoto na makwabtaka da jihar Zamfara wacce 'yan fashi da barayin shanu suka addaba.