Coronavirus: Gwamnati na raba wa talakawa kudaden rage radadi a Abuja

Bayanan sautiRahoton Buhari Muhammad Fage
An wallafa

Danna alamar lasifika domin sauraren rahoton Buhari Muhammad Fage

Gwamnatin Najeriya ta fara raba tallafin kudi naira dubu ashirin ga marasa karfi musamman a yankunan karkara daga cikin shirye-shiryenta na tallafi da ake kira Cash Transfer.

Gwamnatin ta ce tana bada kudin ne domin rage radadin rashi da wasu 'yan kasar ke fama da shi, a wani mataki na yaki da talauci a fadin kasar baki daya musamman wannan lokaci na coronavirus.

Ministar Ma'aikatar Agaji da Ci Gaban Al'umma, Sadiya Umar Farouk ta shaida wa BBC cewa suna bayar da kudin ne ga masu karamin karfi da suka da hada marayu da masu bukata ta musamman da mata marasa karfi da kuma wadanda mazajensu suka mutu.

Ta ce dubu biyar ya kamata a bai wa mutanen amma yanzu gwamnati na raba dubu ashirin ne domin rage masu radadi.

BBC
BBC

"Tun 2016 gwamnati ta fara raba tallafin ga masu karamin karfi, amma saboda coronavirus, shugaban kasa ya bukaci a ninka wa mutane kudaden zuwa N20,000 maimakon dubu biyar, saboda mutane su samu saukin radadin halin da aka shiga," inji Ministar.

Ta kuma ce gidaje sama da dubu biyar ne za a bi ana rabawa mutane kudaden a yankin karamar hukumar Kwali a Abuja.

Ministar ta bayyana cewa sun yi amfani ne da rajistar sunayen mutanen da suka amfana da shirin farko na rage talauci a tsakanin al'umma.

Sannan kuma an ninka tallafin ne domin sake rage musu radadin wahalhalun tattalin arziki da za su shiga sakamakon dokar hana fita domin yaki da coroinavirus.

Wasu mata yayin da suke karbar tallafin gwamnatin Najeriya a Abuja
Bayanan hoto, Gwamnati ta ce ta yi amfani da rajistarta ta baya wurin gano mutanen

Yayin da yake sanar da dokar hana fita a biranen Abuja da Legas da Ogun a ranar Lahadi, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce an ware kudi domin tallafa wa mutanen karkara da ke kusa da garuruwan da dokar ta shafa.

Kazalika ya yi umarni da a daga kafa ga masu biyan bashin kudin tallafi na Tradermoni da MarketMoni da kuma FarmerMoni tsawon wata uku.

Sannan za a yi irin wannan sassauci ga dukkanin basukan da gwamnatin tarayya ta bayar ta hannun Bankin Masana'antu da Bankin Manoma da kuma Bankin Shigarwa da Fitar da Hajoji daga Najeriya.

Har wa yau, Buhari ya ce ya umarci gwamnatocin jihohi da su samar da tsarin ci gaba da bayar da abinci ga 'yan makaranta a wannan lokaci "ba tare da yin karan-tsaye ga dokar yi wa juna tazara ba".

Attajiran Najeriya ma ba a bar su a baya ba

Shugaba Buhari da wasu attajirai a Najeriya
Bayanan hoto, Shugaba Buhari da wasu attajirai a Najeriya

Su ma attajirai da bankuna da manyan kamfanoni a Najeriya sun bayar da gudunmawar biliyoyin naira domin yaki da cutar.

Attajirai irin su Aliko Dangote, Femi Otedola, Abdulsamad Rabiu, Herbert Wigwe da kuma, Segun Agbaje ko wannensu ya bayar da gudunmawar naira biliyan daya don a dakile coronavirus

Mai kamfanin BUA Group, Abdul Samad Rabiu, wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya kara da cewa baya ga kudin, kamfaninsa ya bayar da kayan aiki da suka hada da injina da na'urorin gwaji da sauransu ga jihohi 9 na kasar.