Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Ana bukatar dala biliyan 160 don yaki da cutar
Kungiyar agaji ta Oxfam ta ce ana bukatar tallafin dala biliyan 160 domin hana mutuwar milyoyin mutane sakamakon annobar coronavirus a matalautun kasashe.
Oxfam ta ce kalubalen da ake da shi a kasashen da ke tasowa ya zarta na kasashen da ke da arziki.
Daga cikin misalai da kungiyar ta bayar akwai batun rashin kayan aiki a asibitoci da talauci da kuma rashin dai-daito.
Kungiyar ta yi kiyasin cewa kasashe marassa karfi sai sun rubanya kudaden da suke kashewa a fannin lafiya, sannan ta bukaci a gaggauta soke bashi da tsarin ba da tallafi kai-tsaye.
Oxfam ta ce samar da wadanan kudade za su taimaka wajen bayar da kariya da karin milyoyin ma'aikatan lafiya da samar da gwajin kyauta da kuma magani.
Kungiyar ta agaji ta damu matuka musamman yanayin da ake ciki a sansanonin 'yan gudun hijira da unguwanin marassa galihu, inda ta yi gargadin cewa idan cutar ta shiga za ta yi mummunar illa.
Coronavirus ta kashe sama da mutum dubu 33 a fadin duniya, yayin da fiye da rabin miliyan suka kamu da ita.
A kasashen Afirka ma alkaluman masu kamuwa da cutar na karuwa, wannan dalili ne ya sanya gwamnatoci ci gaba da tsaurara matakan hana bazuwarta.
Kasashen da aka samu karuwar masu dauke da cutar a baya-bayanan sun hada da Iran da ta bayar da sanarawar karin mutum 123 da suka mutu.
A gefe guda kuma, Saudiyya ta rufe birnin Jeddah sannan ta saka dokar hana fita a birnin da za ta fara aiki daga karfe 3:00 agogon kasar, ba karfe 7:00 ba, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar ya rawaito.
A Najeriya alkaluman masu dauke da cutar yanzu haka sun kai 111.