Coronavirus: Fiye da mutum 100 ne ke dauke da cutar a Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC tace yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da coronavirus a kasar ya kai 111.

Sanarwar da hukumar ta NCDC ta fitar a daren Lahadi da misalin 9:30 na dare sun nuna cewa an samu karin mutum 14 da suka kamu da cutar a fadin kasar.

NCDC ta ce daga cikin mutanen, tara a Lagos suke, biyar kuma a babban birnin tarayyar kasar Abuja.

Wannan sanarrwa na zuwa jim kadan bayan shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi jawabi na farko ga 'yan Najeriya kan coronavirus.

Gabanin nan kuma hukumar ta NCDC ta bayyana bullar cutar a jihohin Kaduna da Benue abinda ya kai cewa jihohi uku ne ke fama da cutar a Najeriya.

Tun da farko, gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufa'i ya fito ya bayyana wa jama'a cewa gwajin da aka yi masa ya nuna cewa yana dauke da coronavirus, sai dai alamunta ba su bayyana a jikinsa ba ya zuwa yanzu.

Amma ya ce ya kebe kansa bisa shawarwarin jami'an lafiya.

Gwamna El-Rufa'i ne dai babban mutum na baya-bayan nan da cutar ta shafa zuwa yanzu a Nijeriya, duk da tashi tsayen da aka gani ya yi wajen hana cutar shafar al'ummar jiharsa.

Ya dauki matakai daban-daban ciki har da umarnin hana fita.

Kaduna da Binuwai dai sun zama jihohi na baya-bayan da cutar bulla cikinsu a Najeriya kuma zuwa yanzu cutar ta shiga jiha 11, baya ga babban birnin kasar Abuja.

Gwamnan jihar Legas inda cutar ta fi kamari da mutum 59, Babajide Sanwo-Olu ya ce suna aiki cikin juriya don katse yaduwar annobar a jiharsa musamman a tsakanin mutanen da suka koma gida daga kasashen waje.

A karshen wannan mako, matakin rufe kan iyakokin jihohi da dama a kasar ya fara aiki.

Jihohin Kano da Katsina da Zamfara da Kebbi da Sokoto duk sun hana shiga ko fita ta iyakokinsu.

Sun dai nemi mutane su nisanci shiga duk wani taron jama'a, maimakon haka a zauna a gida, har a ga karshen wannan masifa

Ga jerin jihohin da cutar ta bulla da kuma yawan mutanen da ta harba:

Lagos- 68

Abuja- 21

Ogun- 3

Enugu- 2

Ekiti- 1

Oyo- 7

Edo- 2

Bauchi- 2

Osun-2

Rivers-1

Benue- 1

Kaduna- 1

Har yanzu dai hukumar ta ce mutum daya ne ya mutu sanadin coronavirus a Najeriya, sai mutum uku da aka sallama daga asibiti.

Hukumar ta NCDC ta bayyana cewa a ranar Lahadi ne za a samar da karin cibiyar gwajin coronavirus a Abakaliki babban birnin jihar Ebonyi a kudu maso gabashin Najeriya.

NCDC ta kara da cewa a yanzu, an kara yawan dakunan gwaje-gwajen da ake da su a kasar zuwa 6 har da dakin gwaji na asibitin koyarwa na jami'ar Ibadan.

Jihohin da ake da dakunan gwaje-gwajen sun hada da Legas da Edo da Osun da Ibadan da Abuja babban birnin kasar.