Hotunan yadda masallatan duniya suka kasance a ranar Juma'a

Asalin hoton, Getty Images
Yadda wasu Musulmi suka yi sallar Juma'a a masallacin Al Akbar da ke birnin Surabaya a gabashin tsibirin Java na kasar Indonesiya ranar Juma'a.

Asalin hoton, Getty Images
Yadda cikin babban masallacin garin Moscow da ke kasar Rasha ya kasance a ranar Juma'a 27 ga watan Maris. Akasarin Musulman kasar sun saurari hudubar Juma'a ne ta intanet

Masallacin Annur kenan da ke unguwar Wuse Abuja Najeriya a ranar Juma'a. An rufe masallacin ne sakamakon umarnin da gwamnati ta bayar na dakatar da sallar Juma'a domin dakile yaduwar cutar coronavirus.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu masallata kenan ke layin wanke hannu kafin shiga masallaci a kasar Indonesiya. Duk da fatawar da malaman kasar suka bayar na dakatar da sallar Juma'a, masallatai da dama sun gudanar da sallar.

Yadda wani masallacin Juma'a a Kano da ke Najeriya ya yi cikar kwari yayin sallar Juma'a

Asalin hoton, Getty Images
Wani yaro Musulmi kenan a garin Delhi da ke Indiya tsaye gaban kofar wani masallaci da aka rufe saboda coronavirus.

Asalin hoton, Getty Images
Wani dan kasar Indonesiya kenan ke addu'a a ranar Juma'a a masallacin Al Akbar da ke birnin Surabaya a gabashin tsibirin Java na kasar Indonesiya ranar Juma'a.





