Covid-19 : Mutum uku sun sake kamuwa a Najeriya, Mutum na biyu a Nijar

Asalin hoton, Getty Images
An samu sabbin mutum uku da suka kamu da coronavirus a Najeriya.
Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasar NCDC ce ta wallafa hakan a shafinta na twitter inda ta ce mutanen dukkansu a Legas suke.
Hukumar ta ce mutanen ba su jima da dawowa daga kasashen da cutar ta yi kamari ba.
NCDC, ta shawarci duk wanda ya san ya dawo kasar daga ketare a makonni biyu da suka gabata da ya killace kansa.
Ya zuwa yanzu dai adadin wadanda suka kamu da cutar a kasar ya kai ashirin da biyar inda aka sallami mutum biyu daga cikinsu bayan sun warke.

A Jamhuriyar Nijar kuwa, an kara samun mutum na 2 da ke dauke da coronavirus.
Mutumin dai dan kasar Italiya ne da ke aiki da wata kungiya mai zaman kanta a kasar.
Hukumomi a kasar sun ce mutumin ya shiga kasar ne tun a ranar 28 ga watan Fabrairun da ya gabata amma bai nuna alamar cutar ba sai a ranar Asabar.
Wannan ne dai karo na biyu da aka samu wani mai dauke da coronavirus a Nijar, mutumin na da shekaru sama da hamsin a duniya kuma ya je kasar ne sama da mako biyu daga Italiya.
Ministan lafiya na kasar Dakta Idi Mai Nasara ya shaida wa BBC cewa, tuni aka garzaya da mutumin zuwa asibiti inda ya ke karbar magani, kuma tuni aka killace wasu mutum saba'in da shida da suka yi mu'amala da mutum na farko da ya kamu da cutar a kasar.
Sannan, an kuma killace wasu mutum uku da suka fito daga Italiya inji ministan lafiyar.

A wani labarin kuma, an samu mutum na farko da ya mutu sakamakon cutar coronavirus a Ghana.
Sannan a wani mataki na dakile yaduwar cutar a kasar wadda a yanzu haka akwai mutum fiye da 20 da suka kamu, daga ranar Lahadi ne za a rufe iyakokin kasar zuwa nan da makonni biyu, sannan kuma za a rinka killace duk wasu baki da zarar sun isa kasar.
Haka Uganda ma ta samu mutum na farko da ya kamu da cutar.
Mutumin dai dan kasar ne wanda ya dawo daga Dubai.
Shugaban kasar Yoweri Museveni, ya sanar da cewa daga ranar Lahadi za a dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na fasinja sannan za a takaita dukkan tafiye-tafiye ta sama da ta kasa har ma da ta ruwa a wani mataki na dakile yaduwar cutar.
Uganda dai ita ce kasar Afirka ta baya-bayan nan da aka samu bullar cutar coronavirus.











