Mutum 10 sun sake kamuwa da coronavirus a Nigeria

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ma'aikatar lafiya ta Najeriya ta tabbatar da mutum 10 da suka sake kamuwa da cutar coronavirus a kasar.

Uku daga cikin wadanda suka kamu a Abuja suke, babban birnin kasar, sauran bakwai suna Jihar Legas.

Dukkanin wadanda suka kamu da cutar 'yan Najeriya ne, yayin da tara daga cikinsu suka je kasashen waje a kwanan nan.

Ma'aikatar ta ce wannan ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar zuwa 22 a Najeriya.

Tara daga cikin masu dauke da cutar sun je kasashen Canada da Faransa da Netherlands da Spain da kuma Birtaniya kuma sun shigo Najeriya ne a mako guda da ya gabata.

Shi kuma na 10 din ya harbu ne daga wani wanda ya kamu da cutar a kwanakin baya.

Ukun da suka kamu a Abuja ana kula da su ne a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Abuja da ke Gwagwalada.

Mutum bakwai na Legas kuma suna asibitin kula da cutuka masu yaduwa na Yaba, inda ake kula da sauran wadanda ke fama da cutar.

"A yau Asabar 21 ga watan Maris na 2020, mutum 22 ne aka tabbatar sun kamu da Covid-19, an sallami biyu daga ciki sannan kuma babu wanda ya mutu a Najeriya," in ji Ma'aikatar Lafiyar Najeriya, a wata sanarwa da ta fitar.

Ta kara da cewa ana ci gaba da bin sawun wadanda ake zargin sabbin masu cutar sun yi mu'amala da su.

"Ma'aikatar Lafiya na kara sa ido a dukkanin mashigar Najeriya ta sama da ta ruwa da ta kan tudu sannan ta shimfida ka'idojin da kwamitin shugaban kasa na musamman kan dakile Covid-19 ya bayar," in ji sanarwar.