Ra'ayi Riga: Takaddama kan kudaden tallafi a Najeriya saboda coronavirus

An wallafa

Yanzu haka dai takaddama ta kaure a Najeriya game da makudan kudaden da gwamnatin Najeriya ta ce ta ware domin rabawa masu karamin karfi da nufin rage musu wahalhalu yayin da suke kulle a gida bayan hukumomi a wasu sassan kasar sun umarci mutane kada su fita a kokarinsu na hana bazuwar coronavirus.