Abin da ba ku sani ba kan fashewar batutun mai na Lagos

fashewar batutun mai na Legas
An wallafa

A ranar Lahadi da safe 15 ga watan Maris din 2020 ne aka samu fashewar bututun man fetur a unguwar Abule-Ado da ke birnin Legas a kudancin Najeriya.

A yayin da aka yi amanna cewa wani abu ne ya fashe har ya yi sanadin da gine-ginen da ke kusa suka rushe tamkar hotunan yadda bam ke tarwatsa gini a kasar Syria, tambayar da kowa ke yi ita ce, "Me ya jawo hakan?''

Gwamnatin jihar ta kafa kwamitin da ta dora wa alhakin gano dalilin faruwar hadarin.

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya yi alkawari cewa za a sanar da mutane sakamakon binciken kwamitin.

Inda lamarin ya faru

Yankin da lamarin ya shafa ya fara ne daga titin Adegbola Olujobi zuwa titin Otunba Gani Adams da ke Abule-Ado.

Waje ne da gidajen jama'a suke da kuma Kwalejin 'Yan mata ta Bethlehem da aka sani sosai a yankin.

Wata cibiyar iskar gas ta kamfanin NIPCO na daidai mahadar titin Adegbola Olujobi da kuma titin Gani Adams.

Akwai kuma wani babban bututun mai a yankin.

Me ya faru?

taswira

Bayanan shaidu sun nuna cewa fashewar ta faru ne da misalin karfe 8 zuwa 9 na safiyar Lahadi.

Iyalai da dama a kusa da unguwar sun tafi coci a lokacin, sannan daliban Kwalejin 'Yan mata ta Bethlehem suna cocin cikin makaranta don gabatar da ibadar safe.

Daya daga cikin shaidun da ke zaune a yankin ya shaida wa BBC cewa zai tafi coci don ibadar safe da karfe 9 a lokacin da ya ji warin iskar gas mai tsanani.

"Sai na ce bari na je na gaya wa Rabaran, amma a lokacin da na isa wajen masu tsaro, tuni warin gas din ya mamaye ko ina," in ji shi.

Ya ce ya nan da nan ya yanke shawarar garzaya wa wajen da dalibai suke don taimaka wa wajen ceton su.

"Ba abu ne mai sauki ba," ya ce kafin ya kara da cewa sai ya dauki babur don zuwa yagaya wa rabaran din amma sai wuta ta tashi kafin ya isa, ''Wata wuta da ke ci a wani kantin cin abinci da ke gefen titi ya hadu da iskar gas din sai kawai muka ji wata kara gbuoa!''

Mutumin, wanda bai fadi sunansa ba, ya yi amanna cewar da iskar gas din ta kara yin nisa da munin lamarin sai ya fi haka.

Shugaban karamar hukumar Amuwo Odofin Mr Valentine Buraimoh, wanda ya yi magana da BBC a wajen da abin ya faru sa'o'i kadan bayan hakan, ya ce lamarin ya faru ne sakamakon fashewar wani bututu saboda ''matsalar na'ura.''

Wata babbar mota ta makale a kwata

Wani ganau din shi ma hakan ya ce sai dai ya kara da cewa wata babbar mota ce da ta makale a kwata a kan babban titin Adegbola Olujobi ta fasa bututun a kokarinta na fita daga kwatar, lamarin da ya jawo iskar gas ta fara fita har ta yadu.

Wannan bayani da ya yi ya yi daidai da wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta da ke nuna babbar motar a kusa da gas din.

ganau

Abin da ya biyo baya

A tsakanin rusassun gine-gine da wajen da mutane suka rasa rayukansu, babbar motar da ake zargi da jawo barnar ce kwance kusa da ramin da ke ci gaba da cin wuta da hayaki, kwana biyu bayan fashewar bututun.

An ci gaba da aikin ceto da neman mutane inda aka samu gawarwakin 20 da kuma mutum 25 da suka jikkata.

Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Legas LASEMA da ta kasa NEMA, suna bakin kokarinsu wajen gano abin da ya jawo lamarin da irin barnar da aka samu a wajen.