Kotu ta bai wa Muhammadu Sanusi damar zuwa ko ina ban da Kano

Kotu ta umarci a bai wa Sarki Muhammadu Sanusi II damar shiga ko ina a Najeriya ban da jihar Kano.
Haka kuma kotun ta bayar da kwana uku a bai wa wannan hukuncin da aka yanke ga wadanda aka kai karar kuma su yi aiki da ita.
Wadanda aka kai karar sun hada da hukumar tsaro ta farin kaya, da sufeto janar na 'yan sandan Najeriya, da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS da kwamishinan shari'a na jihar Kano da kuma ministan shari'a na Najeriya.
An dage zaman kotun sai ranar 26 ga wannan watan na Maris.

El-Rufa'i ya ziyarci Sanusi a Awe

Asalin hoton, El Rufa'i
A hannu guda kuma, a ranar Gwamnan jihar Kaduna da ke Najeriya, Malam Nasir El-Rufai, ya tafi garin Awe na jihar Nasarawa domin ganawa da Malam Muhammadu Sanusi na II a ranar Juma'ar.
Hotunan da gwamnatin jihar Kaduna ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Juma'a sun nuna gwamnan a cikin mota inda ta ce yana kan hanyar zuwa garin Awe.
Muhammadu Sanusi II da Nasir El-Rufai sun shafe kusan shekara arba'in a matsayin abokai.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
A ranar Litinin ne gwamnatin jihar Kano ta cire Sarki Sanusi na II daga kan mulki bayan ta zarge shi da rashin biyayya da kuma kin bin umarnin gwamnan jihar.
A ranar ne kuma aka dauki tsohon sarkin a jirgi mai saukar ungulu zuwa garin Loko da ke jihar ta Nasarawa.
Sai dai washegari an mayar da shi garin na Awe, inda ya kasance tun ranar.
Ranar Alhamis rahotanni sun yadu cewa Gwamna El-Rufai ya je garin na Awe domin ganawa da tsohon sarkin, ko da yake BBC ta samu tabbacin cewa gwamnan bai ziyarci sarkin ba.

Wane ne Sarki Muhammadu Sanusi II?
- An haife shi a zuriyar sarakunan Fulani a ranar 31 ga watan Yuli 1961.
- Jika ne ga sarki Sanusi da aka sauke daga gadon sarauta.
- Ya samu digiri a fannin tsimi da tanadi da fannin addini Musulunci.
- An nada shi mukamin gwamnan Babban Bankin Nigeria (CBN) a watan Yuni 2009.
- Mujallar Banker ta bayyana shi a matsayin gwarzon shekara a 2010.
- An dakatar da shi a watan Fabrairu bayan sun samu sabani da shugaban kasa.
- An kuma nada shi a matsayin Sarkin Kano ranar 8 ga watan Yuni 2014.
- Sunansa ya canja daga Sanusi Lamido Sanusi zuwa Muhammad Sanusi II.
- An sauke shi daga kan mulki ranar 9 ga watan Maris na 2020

Kazalika wasu rahotanni sun bayyana cewa an kai Muhammadu Sanusi na II jihar Lagos, amma wani mai tamaka wa tsohon sarkin ya tabbatar wa BBC cewa babu gaskiya a labarin.
Gwamnati jihar Kaduna ta bai wa Muhammadu Sanusi na II mukamai biyu cikin kasa da kwana biyu bayan sauke shi daga kan sarauta.
Da farko gwamnatin jihar ta nada shi a matsayin mataimakin shugaba a majalisar magabata ta hukumar bunkasa zuba jari ta jihar wadda ake kira KADIPA.
Daga bisani kuma aka ba shi mukamin Uban Jami'ar jihar Kaduna.









