Tarihin rayuwar tsohon shugaban Masar, Hosni Mubarak

Asalin hoton, Getty Images
Hosni Mubarak soja ne, kuma shi ne wanda ya daukaka matsayin kasarsa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya.
A karkashin shugabancinsa, Masar ce a sahun gaba wajen kokarin tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin Isra'ila da Falasdinu.
Ya shafe shekaru 30 kan mulki, inda a 2011 ne aka sauke shi bayan juyin juya halin kasar Masar.
Ya fuskanci suka kala-kala saboda amfani da dokar ta baci wajen murkushe abokan hamayya.
An haifi Muhammad Hosni Said Mubarak a ranar 4 ga watan Mayun 1928 a Kafr-El Meselha da ke arewacin Masar.
Duk da kasancewar bai fito daga gidan masu hali da shuni ba, Mubarak ya yi karatu inda ya kammala karatunsa a makarantar sojoji ta Masar a 1949.

Asalin hoton, Getty Images
Mubarak ya shafe shekaru biyu yana tuka jirgin yaki, sannan daga baya kuma ya zama mai horar da sojojin sama.
Marigayin ya kuma shaida yadda aka yi wa Janar Gamal Abdel Nasser juyin mulki a 1952 da kuma rikicin da ya biyo baya.
A 1959, Mubarak ya je tarayyar Soviet babbar mai sayar wa da Masar kayan yaki inda ya koyi yadda ake tuka jirage masu ruwan bama-bamai.
Ya auri Suzanne, a lokacin tana da shekara 17 kuma likita ce, sai kuma ya kara samun girma inda ya zama shugaban makarantar horar da sojojin sama daga nan kuma sai ya zama shugaban sojin rundunar sama ta kasar Masar a 1972.
Yadda ya zama gwarzo
Bayan ya zama shugaban rundunar sojin sama ta Masar, sai aka kuma ba shi mukamin mataimakin ministan tsaro na kasar.
Daga nan ne ya fara suna, saboda yana da kwarewa a bangarori da dama.
Mubarak ya kware wajen shirya yadda za a kai harin ba zata kan dakarun Isra'ila.
Rasha da Amurka sun kusa afkawa cikin rikicin manyan kasashen duniya a yunkurin su na kai dauki ga kawayensu, to amma Isra'ila ta dakile wannan mamayar inda daga karshe ta mayar wa da Masar Sinai.

Asalin hoton, Getty Images
Bayan shekara biyu, sai shugaban lokacin Anwar Sadat ya nada shi a matsayin mataimakin shugaban kasa.
Sadat ya kware a wani abu da ya kira manufofinsa na kasashen wajen "masu girgiza mutane". Ya kori mashawartan Rasha 16,000, ya ziyarci Birnin Kudus yayin da yake filin daga, ya kuma ki gana wa da shugabannin Saudiyya.

Asalin hoton, Getty Images
Mubarak ya mayar da hankali a kan abubuwan da suka shafi cikin kasarsa, to amma daga bisani ya fara kulla dangantaka da sauran shugabannin kasashen Larabawa musamman yarima mai jiran gado na wancan lokacin Fahad.
Bai goyi bayan wata yarjejeniyar zaman lafiya ta Camp David da Shugaba Sadat da Firaiministan Isra'ila suka sanya wa hannu ba.
Wannan yarjejeniya ta raba kan kasashen Larabawa, inda har Mubarak ya yi dana sanin gazawar shugaba Sadat wajen kare dangantakarsu da sauran kasashen Larabawa.
A watan Oktoba ne wasu sojoji suka kashe Sadat a yayin wani fareti da aka shirya domin tunawa da nasarar da Sadat din ya samu a rikicin Isra'ila da wasu kasashen Larabawa a 1973.

Asalin hoton, Getty Images
Wadanda suka kashe Sadat sun buya ne a cikin wata babbar mota wadda ta tsaya a kusa da Shugaba Sadat, daga nan sai suka fito suka yi kamar za su kai gaisuwa ga Sadat.
Anan ne sai suka fara jefa gurneti tare da harba bindiga kan cuncurundon mutanen da ke wajen.
Anan ne aka harbi Sadat, aka kuma kai shi asibiti amma bayan sa'o'i biyu ya ce ga garinku nan.
Hosni Mubarak ya ji rauni a wannan lokacin.
Mubarak ya samu nasarar zama shugaban kasa inda ya samu kaso 98 cikin 100 a wani zaben raba gardama da aka yi wanda a lokacin, shi kadai ne dan takara.
Marigayin ya yi alkawarin tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta Camp David, to amma sai dangantaka tsakaninsu da Isra'ila ma ta fi kyau a kan yadda ta ke a lokacin Sadat.
Masar da Saudiyya su ne kasashen Larabawan da suka fi suna, kuma su ke da arziki, sun kuma bi sahun dakarun da ke kokarin rage wa Ayatollah Khomeini na Iran karfin iko.
A shekarar 1979 ne, aka cire Masar daga cikin kungiyar kasashen Larabawa.

Asalin hoton, Getty Images
Mubarak ya yi karatunsa a makarantar sojoji da ke tarayyar Soviet sannan ya iya yaren Rashanci, to amma ya fi kulla dangantaka tare da kasashen yamma.
Rawar da ya taka wajen tabbatar da zaman lafiya a tsakanin Isra'ila da Falasdinu, ta sa ya kulla dangantaka da shugaban Amurka na wancan lokaci wanda ya aika mishi kayan agaji na biliyoyin daloli.
Anan ne aka rinka sukarsa a kan cewa ya zama dan amshin shatan Amurka.
Ya kara fadada harkokin tsaron kasarsa, sannan ya tsallake hare-hare wajen shida da aka kai masa amma ya samu rauni a wani yunkurin kashe shi da aka yi da wuka.
Mamayar da Iraki ta yi wa Kuwait a 1991, wani nakasu ne ga Mubarak wanda ya jaddada cewa ya samu tabbaci daga Saddam Hussain a kan cewa ba shi da wannan shirin.

Asalin hoton, Getty Images
Saddam ya yi kira da a hambarar da gwamnatin Masar a wancan lokaci, amma kuma sai Amurka ta biya mata bashin biliyoyin daloli sannan ta kara samun masu zuba jari.
Guguwar sauyi ta kasashen larabawa
A watan Janairun 2011, Masar ta balle wajen zanga-zanga. An shafe makwanni ana zanga-zanga, kuma wadanda suke cikin talauci da rashin aikin yi da kuma wadanda suka gaji da mulkin kama karya ne suka fito zanga-zangar.
Alkawarin da yayi na kin tsayawa zabe a zaben shugaban kasa bai gamsar da 'yan kasar ba. Bayan an shafe kwanaki 18 ana zanga-zanga, Mubarak ya dauki shawarar sauka daga mulki.

Asalin hoton, Getty Images
Bayan watanni hudu, Mubarak wanda ba shi da lafiya aka umarce shi da ya je kotu a kan tuhumar da ake masa, ya kuma je ne a kan gadon asibiti inda ya fuskanci tuhume-tuhume da suka hada da na cin hanci da kuma hannu a kisan masu zanga-zanga.
A lokacin, lauyoyin da ke kare shi sun hakikance cewa shugaban kasa ne a shari'ance.
A watan Yunin 2012 ne aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai saboda gazawarsa wajen kare kisan masu zanga-zanga, amma an wanke shi daga sauran tuhume-tuhume.

Asalin hoton, Getty Images
A shekarar 2017 ne, aka wanke shi daga zargin kisan masu zanga-zanga, sannan aka sake shi.
A iya tsawon lokacin da ya shafe yana mulki, kasar Masar ta kasance cikin zaman lafiya, amma kuma ana sanya mutane a kurkuku ba tare da hukunci ba gami da azabtarwa.











