Isra'ila ta kai hare-haren sama Gaza da Syria

A ball of fire is seen following an Israel air strike at Rafah in the southern Gaza Strip on 23 February 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Isra'ila ta kai hare-haren sama Gaza da Syria
An wallafa

Sojojin Isra'ila sun kai hare-haren sama kan kungiyar masu tayar da kayar baya ta Falasdinu (PIJ) a Gaza da Syria a wani martani na harin roka da aka kai wa kasar.

Fiye da rokoki 20 aka harba kudancin Isra'ila daga Gaza a ranar Lahadi, abin da ya jawo barna.

Cikin dare ne kuma sojojin Isra'ila suka kai wasu hare-hare kan mayakan PIJ, da suka hada da wajen da suke kera makamai da sansanin horonsu da ke Damascus.

PIJ ta ce an kashe mayakanta biyu a Syria, kuma ta sha alwashin ramuwa kan kisan nasu.

Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta ruwaito cewa an ji wa wasu Falasdinawa hudu rauni a yankin.

An harba wasu rokokin 14 a ranar Litinin a kudancin Isra'ila, amma an dakile 12 daga cikin su, a cewar sojin Isra'ila. Sai dai rahotanni sun ce ba a samu jikkata ba.

Tashin hankalin ya kara ruruwa a ranar Lahadi da safe, a lokacin da Rundunar Dakarun Tsaron Isra'ila ta IDF ta ce ta kashe wani mayakin PIJ a kusa da kan iyakar kasar da Zirin Gaza.

IDF ta ce dakaru sun gano mutum biyu na kokarin dasa wani bam a kan katangar sai suka bude musu wuta.

Wani bidiyo da aka yada shi a shafukan sada zumunta ya nuna wata motar katafila tana tula wa gawar mutumin kasa, abin da ya harzuka Falasdinawa.

IDF ta ce ta tone gawar saboda ta kare dakarunta daga shiga hadari. Amma sa'o'i kadan sai wasu Falasdinawa suka yi kira da daukar fansa, inda aka harba rokoki da dama daga Gaza zuwa kudancin Isra'ila.

IDF ta ce an dakile rokoki 16 amma wasu guda goman sun fada kan dandaryar kasa.

A picture shows the smoke trail of a rocket, fired by Palestinian militants, over the Gaza Strip

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An harba fiye da rokoki 20 daga Zirin Gaza a ranar Lahadi

Kafofin yada labaran Isra'ila sun ruwaito cewa harin ya lalata gida daya da mota daya, sannan an kai wasu mutum biyu da suka ji rauni asibiti a Ashkelon - wata mata ta ji rauni a kanta a yayin da take gudun ceton rai, sai kuma wata matar da ta suma.

PIJ ta dauki alhakin kai harin rokar, inda ta ce hakan martani ne kan kisan mayakinta a kan katangar kan iyaka.

A ranar Lahadi da daddare, wasu jiragen yakin Isra'ila sun kai hare-haren ramuwa kan wuraren PIJ.

IDF ta ce wuraren da aka kai harin a Gaza sun hada da hedikwatar kungiyar da ke kudancin birnin Khan Younis, da kuma wuraren ajiyarta a Rafah mai makwabtaka.

A Syria kuwa, an kai harin ne wani sansani da PIJ ke amfani da shi wajen samar da sabbin makamai take kuma samar da kilogiram 10 na man da ake sawa a roka duk wata, a cewar IDF.

Sannan IDF ta ce harin ya samu wata tawagar PIJ da ke shirin harba rokoki daga arewacin Gaza.

Light in the sky above Damascus during Israeli air strikes on Palestinian Islamic Jihad targets in Syria (24 February 2020)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta dakile mafi yawan hare-haren rokar