Abin da ya sa muka mika wa Isra'ila birnin Kudus - Trump

Shugaba Trump tare da Praministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Bayanan hoto, Trump ya ce "idan Falasdinawa suka rungumi zaman lafiya to duniya za ta so su"
An wallafa

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce gwamnatinsa ce ta fi dacewa ta sasanta dadaddiyar takaddamar da ke tsakanin Falasdinawa da Isra'ila.

Donald Trump ya shaida hakan ne yayin da yake bayyana shirin Amurka na samar da zaman lafiya mai wanzuwa a yankin Gabas ta Tsakiya a fadar White House da yammacin Talatar nan,

Shugaba Trump wanda Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ke tsaye a gefensa, ya ce matakin da gwamnatinsa ta dauka na mika 'Tuddan Golan' da kuma ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila na da alaka da irin son zaman lafiyar da Amurka ke son ganin wanzuwarsa a yankin.

Ya mika tayin sasantawa ga Falasdinawa da shugabanninsu, yana cewa Amurka za ta ci gaba da tsayawa a tsakiya don tabbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ya kama sunan shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas karara, yana cewa: "Ka sani idan kuka rungumi sasanci da zaman lafiya kasashen duniya za su so ku sannan za su mara maku baya domin ci gaban kasarku."

"Abin kasarku ke samarwa zai ninka sannan tattalin arzikinku ya hauhawa... babu wanda za a raba da muhallinsa tsakanin Falasdinawa da Yahudawa."

Mista Trump ya kuma ce binin Kudus "zai ci gaba da zama babban birnin Isra'ila halak malak".

A nasa jawabin, Benjamin Netanyahu ya ce Amurka ce gatan Isra'ila.

"Zan ci gaba da nuna godiyata ga shugaba Trump har ranar kiyama bisa wannan gata da ya yi wa Isra'ila," in ji Netanyahu.

Wasu daga cikin jakadun kasashen Gabas ta Tsakiya sun halarci taron.