An gano hanyar mayar da gawa taki

Asalin hoton, Recompose
- Marubuci, Daga Pallab Ghosh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC na Kimiyya, BBC News, Seattle
- An wallafa
Wani kamfanin Amurka ya ce ya gano wata hanya da za a iya mayar da gawar mutum taki don kare yanayi da muhalli.
Kamfanin mai suna Recompose ya ce mayar da gawa taki zai sa a adana sama da tan daya na iskar carbon, idan aka kwatanta da kona gawa ko kuma binne ta yadda aka saba.
Kamfanin ya ce nan da shekara guda zai gudanar da jana'izar mayar da gawa taki a karon farko a jihar Washington.
Shugabar kamfanin Recompose, Katrina Spade ta ce fargabar da ake da ita kan sauyin yanayi yasa mutane da yawa ke nuna sha'awar wannan sabuwar kirkira.
"Kawo yanzu mutane 15,000 sun nuna sha'awarsu. Kuma dokar da za ta ba mu damar yin wannan aiki a wannan jiha ta samu goyon bayan jam'iyyu biyu don haka an fara duba ta," a cewarta.

Asalin hoton, Recompose
Ta ce ta yi tunanin fara wannan shirin ne shekara 13 da suka gabata lokacin da tunanin mutuwarta ya zo mata - lokacin tana da shekara 30.
"Idan na mutu, wannan duniyar da ta ba ni kariya kuma ta ba ni tallafi tsawon rayuwata, bai kamata in yi wani abu in saka mata ba idan na tafi?
"Tunani ne mai kyau."
Shirin ya kunshi kwantar da gawar a wani rufaffen wuri da kananan itatuwa, da wani ganye mai suna alfalfa da kuma ciyawa. Za ai ta jujjuya ta a hankali don bai wa sinadarai damar rubar da ita.

Asalin hoton, Recompose/MOLT Studios
Bayan kwana 30, sai a bai wa dangin mamacin takin don su zuba wa tsirrai.
Duk da tsarin ba shi da wahala, an kwashe shekaru hudu ana bincike don a kware a kansa.
Duk wanda ya so zai iya shiga wannan shiri amma a jihar Washington ne kawai ake da izinin yinsa.
Mis Spade ta ce ta yi imani nan da dan lokaci zai samu karbuwa a sauran jihohin Amurka da ma sauran kasashen duniya.









