Coronavirus: China ta kori manyan jami'ai saboda gaza magance cutar

Asalin hoton, Getty Images
China ta kori manyan jami'anta daga mukaminsu saboda yadda suka gaza wajen magance barkewar annobar Coronavirus yayin da alkaluman wadanda suka mutu suka zarce 1,000.
Babban sakataren jam'iyyar a hukumar lafiya ta lardin Hubei da shugaban hukuymar na cikin wadanda suka rasa mukamansu.
Sune manyan jami'ai da kawo yanzu suka rasa ayyukansu, amma a baya ma an kori wasu ma'aikata a mataki daban-daban.
Mataimakin shugaban kungiyar Red Cross a birnin ma ya rasa aikinsa saboda "watsi da aiki" kan yadda ake karban kudade da kayan agaji.
A rana Litinin, mutum 103 suka rasa rayukansu a lardin Hubei kawai, wanda wannan ne adadi mafi yawa tun da annobar ta barke a China.
Kawo yanzu mutum 1,016 ne suka rasa rayukansu a fadin kasar.
Amma an sami raguwar wadanda suka kamu da cutar da misalin kashi 20 cikin 100 idan aka kwatanta da ranar Lahadi, daga 3,062 zuwa 2,478.





