Indiya ta amince damisa su dawo kasar

An wallafa

Babbar kotun Indiya ta ce za a iya sake dawo da damisu kasar, shekara 70 da batar da su baki daya.

Kotun kolin kasar ta na maida martani ne kan rokon da gwamnati ta yi na a sake dawo da su, inda ta ce za a iya yin hakan amma dazuka za su zama matsugunansu da kuma za a duba inda ya dace su rayu.

Damisa dai dabbace mai cutarwa ga bil'adama, kuma baki daya wadanda suka rage a doron kasa guda 7,100 ne yawanci su na Afirka.

A baya, nau'in damisar da ake samu a yankin Asiya sun taba zama a Indiya, amma a yanzu a kasar Iran kadai ake ganin irinta wadda baki daya guda 50 ne suka rage.

Kotun kolin India ta ce dole sai an gabatar da dabbar ta hanyar amfani da dabarun zamani, dan gano ko za ta iya rayuwa a yanayin kasar.

Binciken kwararru, ya gano an kashe akalla Damisa 200 a India, yawanci kuma makiyaya da ke kiwon raguna da akuya ne suka kashesu a zamanin turan mulkin mallaka.

Ita ce kadai dabbar da ta yi wuyar gani bayan kasar ta karbi 'yancin kai a shekarar 1947.

Tsohon ministan Muhallin kasar Jiram Ramesh, ya yi marhabin da matakin sake dawo da Damisa Indiya.

Sama da shekara 10 kenan, masu kare hakkin dabbobi da kungiyoyi masu zaman kansu da kwararru kan halayyar dabbobin ke ta tattaunawa dan ganin yadda za a sake dawo da nau'in damisar Indiya.