Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana fasa kwaurin Damisa zuwa kasashen Larabawa
BBC ta gano cewa ana fasa kwaurin damisa daga Habasha zuwa kasashen Larabawa.
Tsananin bukatar damisa musamman nau'in 'Rabbi' daga hamshakan masu arziki a Gabas ta Tsakiya ya sa an fara fasa kwaurin dabbar daga Habasha.
Wani ma'aikacin gandun dajin Habasha ya fada wa BBC cewa duk wata akalla damisa hudu ake shiga da ita ta barauniyar hanya zuwa kasashen musamman Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Ana kuma sayar da su ne ga hamshakan masu arziki a wadannan kasashe.
A cewarsa, duk guda daya ana iya sayar da ita a kan dalar Amurka 10,000.
Kuma masu kudin na sayen ta ne kawai domin sha'awa da kuma kawata gidajensu.
Bincike ya nuna cewa nau'in damisar da aka fi bukata don kawata gidajen masu arziki da ake kira 'Cheetahs' guda 7,100 ne suka rage a duniya.
Kuma kashi 90 daga ciki suna zaune ne a yankin Afirka.
Haka ma binciken ya gano cewa daga Habasha ana bi ta yankin Somaliland ne da su, kafin a ketara Yemen daga nan kuma sai a shiga da su Saudiyya da Hadadddiyar Daular Larabawa.
A yanzu dai kungiyoyin da ke rajin kare dabbobi na fargabar nan ba da jimawa ba nau'in damisar zai zama tarihi a doron kasa, ganin irin yadda ake fasa kwaurin nata.