Khamenei ya nemi a yi wa sojojin Iran uzuri

Ayatollah Ali Khamenei

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ayatollah Ali Khamenei ne shugaban addini a Iran kuma shi ke tafiyar da harkokin siyasar kasar
An wallafa

Shugaban addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei Khamenei ya kare sojojin kasar bayan amincewa da harbo jirgin kasar Ukraine bisa kuskure.

Ali Khamenei ya ce "sojojin kasar na taka muhimmiyar rawa wajen tsare Iran".

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna fushi kan jirgin fasinjar Ukraine da sojin Iran suka harbo bisa kuskure a makon da ya gabata.

Hakan na nufin shugaban addinin na nema wa sojojin uzuri ga 'yan kasar da suke kara matsa wa gwamnati lamba kan faruwar al'amarin.

Haka zalika, Ayatollah Khamenei ya jagoranci sallar Juma'a a babban birnin Tehran - karon farko da ya yi haka cikin shekara takwas.

Shugabannin Iran na fuskantar matsin lamba sakamakon tabarbarewar tattalin arziki a kasar saboda takunkuman da Amurka ta kakaba mata.

A ranar Laraba, Shugaba Hassan Rouhani ya yi kira da a samu hadin kai a fadin kasar.

Jirgin Ukraine din kirar Boeing 737-800 na kan hanyarsa ta zuwa Kyiv daga Tehran a ranar 8 ga watan Janairu lokacin da ya yi hadarin jim kadan bayan ya tashi.

Duk fasinjojin cikin jirgin 176 har da Iraniyawa da dama da kuma 'yan Canada sun mutu.

Hukumomin Iran da farko sun musanta suna da hannu a kakkabo jirgin amma daga bisani bayan da kasashen duniya suka matsa lamba, dakarun juyin-juya halin kasar sun amince cewa sun dauka makami me linzami ne.

Sa'oi bayan harbo jirgin, makamai masu linzami na Iran sun kai hari kan wasu sansanonin sojin Amurka a Iraki.

Harin ya zo ne a matsayin martani kan harin da Amurka ta kai da jirgi maras matuki a Bagadaza wanda ya yi sanadiyyar kashe babban sojin Iran Qasem Soleimani.

A ranar Juma'a, Amurka ta ce sojojinta 11 harin ya shafa. Tun da farko ta ce babu wani sojinta da ya jikkata.

Me ke faruwa a Iran?

Kamfanin dillancin labarai na Iran, Mehr ya ce Ayatollah Khamenei mai shekara 80 zai jagoranci sallar Juma'a a wannan makon a masallacin Mosalla da ke Tehran sai dai bai danganta lamarin da abin da ke faruwa ba a kasar a yanzu ba.

Kamfanin na Mehr ya rawaito jami'ai na cewa "Iran za ta sake nuna mahimmancin hadin kanta."

Rabon Ayatollah Khamenei ya jagoranci sallar Juma'a a Tehran tun 2012 lokacin da aka yi bikin cika shekara 33 da juyin-juya hali a kasar.

Ana jagorantar sallar Juma'a a babban birnin kasar ne a lokacin da shugabannin Iran ke da wani muhimmin sako ga jama'a, a cewar Mehdi Khalaji na cibiyar diflomasiyya ta Near East da ke Washington.

Ya kara da cewa a tarihi, shugabannin Iran sun bar wannan aikin ga malamai masu fada a ji.

Labarin kakkabo jirgin da Iran ta yi ya janyo zanga-zanga a wasu biranen Iran musamman jami'oi inda ake kiran dakarun juyin-juya halin da 'makaryata' kuma 'masu kisa'.

Hoton bidiyon da aka wallafa a kafafen sada zumunta a wajen jana'izar sojojin da suka mutu ya nuna mutane na alhini tare da furta kalaman nuna kin jinin gwamnati.

Iran ta cafke masu zanga-zanga da dama kan hadarin jirgin kuma Shugaba Rouhani ya ce wata kotu ta musamman ce za ta jagoranci binciken, yana mai cewa "komai zai gudana a idon duniya."

Ministan harkokin wajen kasar, Mohammad Javad Zarif ya amince cewa an yi wa 'yan Iran "karya" amma ya dage cewa an sa gwamnatin cikin duhu.

Hukumomin Iran sun fuskanci matsin lamba daga bangarori da dama. Kuma tattalin arzikin kasar na ci gaba da fuskantar barazana saboda takunkuman da Amurka ta kakaba mata.

A shekarar da ta gabata, zanga-zanga ta juye zuwa rikici a sassan kasar bayan gwamnati ta sanar da kudirinta na kara farashin mai.

Grey line

Khamenei ya bayyana sha'awar kare dakarun juyin-juya hali

Sharhi da ga Kasra Naji, BBC Persian

Rabon da jagoran addini na Iran ya jagoranci sallar Juma'a a Tehran tun lokacin da aka yi juyin-juya halin da kasashen Larabawa suka yi wato 2012.

A lokacin ya yi amfani da wannan damar wajen yin wa'azi cikin harshen Larabci.

Da alama a yanzu, Ayatollah Ali Khamenei na son kare dakarun juyin-juya hali da ake suka a Iran saboda harbo jirgin Ukraine.

Akwai fargaba cewa yana iya kiran a sa ido kan dalibai da masu zanga-zanga domin kare gwamnatinsa.

Hukumomi sun dauki nauyin zanga-zangar gama gari ranar Juma'a domin nuna goyon baya ga dakarun juyin-juya halin.

A Tehran, akwai shirye-shiryen da ake don samar da dumbin magoya baya don nuna karfin iko.

Sai dai da yawan Iraniyawa 'yan ba ruwana suna son ya amince cewa mulkinsa ba abin da ya haifar sai wahala ga 'yan kasar.

Grey line

Ya batun bincike?

Bayan wani taro a London ranar Alhamis, ministoci daga kasashe biyar da suka rasa 'yan kasarsu a hadarin jirgin sun bukaci hadin kan Iran don gudanar da sahihin bincike.

Ministocin harkokin wajen Afghanistan da Birtaniya da Canada da Sweden da kuma Ukraine su ma sun ce tilas Iran ta biya su diyya.

Da yake magana amadadin ministocin, ministan harkokin wajen Canada, François-Philippe Champagne ya ce "muna nan ne don neman a yi gaskiya da adalci ga mutanen da suka mutu 'yan Ukraine da Sweden da Birtaniya da Afghanistan da Canada da kuma Iran, ta hanyar yin cikakken bincike na gaskiya.

"Akwai tambayoyi da dama, iyalan mamatan na son amsoshinsu, kasashen da suka rasa jama'arsu su ma suna son amsoshi sannan kasashen duniya ma na bukatar amsoshin tambayoyin. Duniya na dakon wadannan amsoshin kuma ba za mu daina magana ba har sai mun same su."

Mr Champagne ya ce ya kamata a hukunta mutanen da suka yi ta'annatin.

A ranar Laraba, masu bincike daga Canada sun ziyarci wajen da jirgin ya yi hadari inda suka gudanar da bincike kan buraguzon ginin.

Suna sa ran shiga cikin masu yin nazari kan na'urar nadar murya, Black Box - wani muhimmin abu da ake dubawa wajen gano hakikanin abin da ya faru ga jirgin da kuma yadda ya yi hadarin.