Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Nasarori 9 da 'yan sanda suka samu a 2019'
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta yi nasara kan abubuwa guda tara a shekarar da ta gabata ta 2019.
Wannan dai na zuwa a dai-dai lokacin da rundunar 'yan sandan ta Najeriya ta sha alwashin gudanar da bincike kan wani faifan bidiyo da ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta, inda aka wasu 'yan sanda na amfani da na'urar cire kudi ta POS domin karbar na goro daga jama'ar gari.
Rundunar ta zayyana abubuwan guda takwas a shafinta na Twitter a ranar Juma'a
Nasarori 9 da rundunar ta ce ta samu a 2019
- Ta samu nasarar kama makamai 2,037
- Ta karbe harsasai guda 20, 870
- Ta kwato ababan hawa da aka sace guda 1,662
- Rundunar 'yan sanda ta kama 'yan kungiyar asiri 1,622
- Ta tsare wadanda ake zargi da kisan kai guda 758
- 'Yan sanda sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su guda 529
- Rundunar ta tsare wadanda ake zargi masu garkuwa da jama'a ne guda 1,527
- 'Yan sanda sun kama wadanda ake zargi da fashi da makami guda 2,626
- Ta kama wadanda ake zargi da laifuka daban-daban a fadin Najeriya guda 6,531.