'Nasarori 9 da 'yan sanda suka samu a 2019'

Mohammed Adamu

Asalin hoton, Twitter

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta yi nasara kan abubuwa guda tara a shekarar da ta gabata ta 2019.

Wannan dai na zuwa a dai-dai lokacin da rundunar 'yan sandan ta Najeriya ta sha alwashin gudanar da bincike kan wani faifan bidiyo da ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta, inda aka wasu 'yan sanda na amfani da na'urar cire kudi ta POS domin karbar na goro daga jama'ar gari.

Rundunar ta zayyana abubuwan guda takwas a shafinta na Twitter a ranar Juma'a

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Nasarori 9 da rundunar ta ce ta samu a 2019

  • Ta samu nasarar kama makamai 2,037
  • Ta karbe harsasai guda 20, 870
  • Ta kwato ababan hawa da aka sace guda 1,662
  • Rundunar 'yan sanda ta kama 'yan kungiyar asiri 1,622
  • Ta tsare wadanda ake zargi da kisan kai guda 758
  • 'Yan sanda sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su guda 529
  • Rundunar ta tsare wadanda ake zargi masu garkuwa da jama'a ne guda 1,527
  • 'Yan sanda sun kama wadanda ake zargi da fashi da makami guda 2,626
  • Ta kama wadanda ake zargi da laifuka daban-daban a fadin Najeriya guda 6,531.