Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwa 9 da Trump ya fada kan Iran a jawabinsa
Da yammacin Laraban nan ne Shugaban na Amurka, Donald Trump ya yi jawabi dangane da harin makami mai linzami da Iran ta kai kan biyu daga cikin sansanonin sojin Amurkar da ke Iraki.
Donald Trump wanda ya yi gajeren jawabi ta gidan talbijin ya nuna cewa babu wadda ya jikkata daga harin na makami mai linzami.
A daren ranar Talata ne dai Iran ta yi luguden makamai masu linzami kan sansanonin sojin na Amurka Irbil da Al Asadda da ke Iraki.
Iran ta ce hare-haren 'ramuwar gayya ne' ga kisan da Amurka ta yi wa janar Qasemi Soleimani ranar Juma'a.
To sai dai Donald Trump ya fito da wasu abubuwa guda tara a yayin jawabin nasa kamar haka:
- Ba a kashe mana ko kaza ba: "Babu sojan Amurka ko na Iraki da ya mutu sakamakon harin makamai masu linzami da kasar Iran ta kai kan sansanin sojin Amurka da ke Iraki ranar Talata."
- Iran na yi mana fatan mutuwa: Gabar da Iran ke nuna mana ta karu ne tun bayan sanya hannu a kan yarjejeniyar da suka kulla a shekarar 2015. Kuma an ba su zunzurutun kudi har dala biliyan 150, ban da ma wanda ba a bayyana ba da suka kai dala dala biliyan daya da miliyan 800. A maimakon su yi wa Amurka godiya, a'a sai ihu suke suna cewa mutuwa ta tabbata ga Amurka.
- Ba lallai sai mun yi amfani da makamai ba: "Mu ne muka fi kowa karfin soja a duniya, inda muke da manyan makamai masu gudun walkiya. Sai dai hakan ba ya nufin lallai sai mun yi amfani da su."
- Ya kamata ya yi mu yi aiki tare Iran: "Kungiyar IS makiyar Amurka ce sannan makiyar Iran ce, saboda haka ya kamata a ce mun yi aiki tare wajen murkushe kungiyar."
- Muna kira a mayar da Iran saniyar ware : Donald Trump ya yi kira ga kasashen Turai da su warware duk wata alaka da ke tsakaninsu da kasar Iran domin mayar da ita saniyar ware ko ta gyara halinta."
- Mai kaunar ransa ba zai kai mana hari ba: "Duk wanda yake kaunar rayuwarsa ba zai yi wa al'umarmu barazana ba Wadannan takunkuman masu tsauri za su ci gaba da zama a kan Iran har sai ta sauya halayenta.
- Wajibi ne Iran ta ajiye shirinta na nukiliyya:
- Soleimani dan ta'adda ne: Donald Trump ya ce "Janar Qasem Soleimani dan ta'adda ne wanda ya dade yana kitsa hare-hare kan al'ummar yammacin duniya wanda kuma ya kamata a ce tuntuni ya mutu."
- Za mu kara wa Iran takunkumi: "Yayin da muke ci gaba da duba irin martanin da za mu mayar, Amurka za ta kara yawan takunkumai kan Iran."