Za a daina yin WhatsApp a wasu wayoyi a 2020

An wallafa

Kamfanin WhatsApp ya ce manhajarsa ba za ta rika aiki a wayoyin da suka kai shekara biyar da kerawa ba.

WhatsApp din wanda mallakin Facebook, ya daina aiki kan wayoyi kirar Windows wadanda Operating System ya tsufa tun daga ranar 31 ga watan Disamba.

Wannan mataki zai shafi wayoyi samfurin Nokia Lumia wadda take amfani da manhajar Windows.

Wayoyi irin Nokia Lumia 650 sun shiga kasuwa ne shekara hudu da suka gabata, amma kuma har yanzu ana amfani da su.

Daga watan Fabrairun 2020, wasu wayoyin kuma da wannan lamari zai shafa su ne Iphone da ke amfani da manhajarr iOS 8 da wayoyin zamani na Android da ke amfani da manhajar 2.3.7.

Tun daya ga watan Yuli mutanen da ke amfani da irin manhajar kamfanin Microsoft wajen sauke manhajoji a wayoyinsu suka daina sauke WhatsApp a wayoyinsu.

Hakan kuma ya zo ne bayan kamfanin na WhatsApp ya gargadi masu amfani da shi kan wayoyinsu na Windows cewa za su lura wani bangare na WhatsApp din ya daina aiki a wayoyinsu.

WhatsApp ya ce duk da matakin ba abin da suka so bane amma hakan shi ne zai sa su bai wa mutane damar sada zumunci da 'yan uwansu.

A shekarar 2018, WhatsApp ya daina aiki a wayoyi samfurin BlackBerry da kuma wadanda manhajarsu ta Window ta zama tsohon yayi.