Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana ce-ce-ku-ce kan shirin janye sojoji wasu sassan Najeriya
Matakin gwamnatin Najeriya na janye dakarun sojin kasar daga wasu yankuna da take ganin an samu nasarar shawo kan matsalar tsaro a cikinsu ya fara janyo ce-ce-ku-ce.
A ranar Litinin ne shugaba Muhammadu Buhari ya gana da hafsoshin tsaron kasar, inda suka tattauna yiwuwar fara janye sojoji daga wasu yankunan kasar domin bai wa 'yan sanda da sauran jami'an tsaron da ba sojoji ba damar tsare yankunan.
Mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu ya ce "matakin wata manuniya ce kan yadda ake samun ci gaba a fannin tsaro a wasu sassan kasar."
Sai dai wasu 'yan kasar da dama da masana na ganin 'yan sanda ba su da karfin da za su tafiyar da sha'anin tsaro ta fuskar karancinsu da kayan aiki.
Gruf Kaftin Sadiq Garba Shehu mai murabus, masanin tsaro a Najeriya, ya ce akwai wasu wuraren da aka samu zaman lafiya da za a iya janye sojoji amma kuma sai an kara wa 'yan sanda karfi.
Ya ce yankunan kasar da aka jibge sojoji kamar jihohin Benue da Filato, ya kamata a janye sojoji su don mayar da su yankin arewa maso gabas na kasar inda aka fi bukatarsu.
"Dama abin da ake so shi ne a raba soji da shiga cikin jama'a matsawar ba wani yakin kasa da kasa ne ya kaure ba, 'yan sanda ya kamata a bari da wannan aiki," In ji shi.
Amma ya ce dole ne gwamnatin ta samar da karin 'yan sanda da kuma ba su isassun kayan aiki matsawar ana so su iya tunkarar aikin matsalar tsaro.
Gwamnatin Tarayya dai ta ce za ta yi nazari kan batun kuma idan ta gamsu da zaman lafiyar da aka samu, "to lalle za ta rage sojoji."
"Wannan ba ya nufin za a janye jami'an tsaro gaba daya ba ne, sojoji za a rage," a cewar Malam Garba Shehu mai magana da yawun shugaba Buhari.
Sai dai bai bayyana yankunan da janye sojojin zai shafa ba tukuna, amma ya ce hakan ba zai shafi yankin arewa maso gabashin kasar ba.
Batun dai ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin 'yan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta inda wasu ke goyon bayan matakin, yayin da kuma wasu ke ganin janye sojoji barazana ga tsaro.
A karshen makon da ya gabata, kungiyar IS a Yammacin Afirka wato ISWAP ta saki wani bidiyon da ta ce ta kashe wasu Kiristoci 11 'yan Najeriya da manufar daukar fansa.
Har wa yau, a ranar Litinin din nan jaridar Premium Times ta wallafa labarin wani sabon harin da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka kai wa kauyen Mandaragirau da ke karamar hukumar Biu ta jihar Borno.
Kusan dukkanin yankunan Najeriya dai na fama da matsalar tsaro, kuma mahukunta sun sha cewa suna iya bakin kokarinsu domin tabbatar da yaki da wannan matsala.
Ko a baya-bayan nan sai da wasu al'umomin kauyuka a yankunan jihar Zamfara suka koka kan yadda mahara ke ci gaba da kai musu hari, duk da yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin jihar ke ikirarin cewa ta cimma da yan bindigar a watannin baya.
Mutanen kauyukan Dankurmi, da Zargado da Danhayin Zargado Farar Kasa da ke karkashin masarautar Dansadau a karamar hukumar Maru sun ce maharan na cin karensu ba babba dauke da makamai, abin da ke razana jama'a.