Za a 'janye' sojoji daga wasu sassan Najeriya

An wallafa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da hafsoshin tsaron kasar a fadarsa da ke Abuja a ranar Litinin.

Ana ganin ganawar ba za ta rasa nasaba da karuwar hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kai wa kauyuka da ma kan sansanin sojoji a yankin arewa maso gabashin kasar.

Shugaban da hafsoshin tsaron sun tattauna yiwuwar fara janye sojoji daga wasu yankunan kasar domin bai wa 'yan sanda da sauran jami'an tsaron da ba sojoji ba damar tsare yankuna.

Mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu ya ce "matakin wata manuniya ce kan yadda ake samun ci gaba a fannin tsaro a wasu sassan kasar."

Ya ce gwamnati za ta bincika batun kuma idan ta gamsu da zaman lafiyar da aka samu, "to lalle za ta rage sojoji."

"Wannan ba ya nufin za a janye jami'an tsaro gaba daya ba ne, sojoji za a rage," in ji shi.

Sai dai bai bayyana yankunan da janye sojojin zai shafa ba tukuna, amma ya ce hakan ba zai shafi yankin arewa maso gabashin kasar ba.

A karshen makon da ya gabata ne dai kungiyar IS a Yammacin Afirka wato ISWAP ta saki wani bidiyon da ta ce ta kashe wasu Kiristoci 11 'yan Najeriya da manufar daukar fansa.

Har wa yau, a ranar Litinin din nan jaridar Premium Times ta wallafa labarin wani sabon harin da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka kai wa kauyen Mandaragirau da ke karamar hukumar Biu ta jihar Borno.

An dai ce maharan wadanda suka yi wa garin tsinke a daren Lahadi sun kona cocin kauyen da wata makaranta sannan kuma sun yi garkuwa da wasu mutane.