Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dandazon mutane sun kalli kusufin rana mai kama da zoben wuta
Al'umma a yankin Asiya sun kalli yadda kusufin rana na shekara-shekara, wanda aka yi wa lakabi da "ring of fire" da Ingilishi - wato ''zoben wuta''.
Dandazon mutanen sun taru domin kallon abin al'ajbin a kasashe dabn-daban ciki har da Sri Lanka, da Indonesia, da Indiya da kuma Saudiyya.
A kusufin da wata ke yi duk shekara, wata yana mamaye tsakiyar rana, inda yanayin ke kama da zobe.
Akalla ana yin kusufin rana sau biyu a kowacce shekara, suna faruwa ne idan inuwar wata ta lullube duniya.
Kusufin rana na baya-bayan nan an yi shi ne a ranar 2 ga watan Yuli, ya kuma fito baro-baro ana gani har a kudancin Amurka.
Ana sa ran kusufin rana na gaba za a gan shi a ranar 14 ga watan Disambar 2020, za kuma a gan shi baro-baro a kudancin kasashen Chile da Argentina da kuma kudu masu yammacin Afirka da Antarctica.