Waiwaye kan abubuwan da suka faru a 2019 a Kamaru

An wallafa

Shekara ta 2019 da take ban kwana, ta shiga kasar Kamaru dauke da rikice-rikice da dama a bangaren siyasa, rayuwar zamantakewar jama'a da wasu harkokin yau da kullum na neman tallafa wa rayuwa.

Rikicin siyasa game da zaben shugaban kasa da ya fara a shekara ta 2018, ya ci gaba da kankane sarari a shekara ta 2019, daga farkon shekarar har izuwa karshenta.

Sakamakon irin hatsaniyar da aka dinga yi tsakanin gwamnati da 'yan siyasa da wasu jama'a fararen hula, hakan ya kai ga Kamaru kasancewa a sahun gaba daga jerin kasashen da takwarorinsu na yammacin duniya masu karfin tattalin arziki da kungiyoyin kasa da kasa masu kare hakkokin bil Adam suka sa wa ido.

1- Wani abinda za a fi tunawa game da Shekara ta 2019 da ta yi ban kwana shi ne kamun kaji da jami'an tsaro na gwamnatin Kamaru suka yi wa tarin magoya bayan jam'iyyar adawa ta MRC, wadda Maurice Kamto ke jagoranta.

A kalla mutum 117 ne suka shiga hannun hukuma bisa ga zargin taka dokar da aka ce sun yi.

Taka dokar ita ce fitowa titin da suka yi suna yunkurin tayar da tarzoma.

Abinda su kuma magoya bayan jam'iyyar suka kira da machi na lumana domin nuna halin mun ki, dangane da irin magudin da suka ce an tafka a zaben shugaban kasa.

2- A yayin da 'yan siyasa suke ta tasu dambarwar, a wani bangaren kuma masu fafutuka da suke yunkurin kafa kasar Ambazoniya a yankin renon Ingila na dada ci gaba da yin dauki ba dadi da dakarun gwamnati.

Ganin cewa madugunsu Julius Ayuk Tabe da wasu mukarrabansa na zaman daurin rai da rai a gidan wakafi, sakamakon wasu laifukan da aka samesu da aikatawa irin na cin amanar kasa da yunkurin yi wa kasa zagon kasa da tayar da tarzoma, da haddasa ayyukan ta'addanci.

Irin ta'asar da suka dinga yi, ta kassara al'amurra a dukkanin fannonin rayuwa kamar harkokin kasuwanci da suka durkushe.

3- A wani fanni mai nasaba da wannan, ta yankin arewacin kasar mai fama da rikicin kungiyar Boko Haram, al'amura ne suka fara daidaita kamar na harkokin kasuwanci bisa ga bayanin da gwamna Mijinyawa Bakary ya yi.

Masu aikin sa kai da ake kira Comite de vigilence ko kuma 'yan kato da gora suma sun bayar da irin tasu gudunmowar domin ganin harkokin tsaro da zaman lafiya sun tabbata a inda suke rayuwa.

4- Sake cillawar da harkokin kasuwanci suka yi ne a tsakanin Kamaru da Najeriya, da Harkokin kasuwanci sun fara daidaita a kan iyakar KAmaru da Najeriya saboda fara wanzuwar zaman lafiyai ga hukumomin kasashen biyu tare da hadin gwuiwar Majalisar Dinkin Duniya, aka fara mayar da 'yan gudun hijiran Najeriya gida, masamman ma mazauna sansanin Minawao a Kamaru.

Ko da yake har a yanzu akwai raguwar dubai a kasa wadanda suke ta yin korafi da har a yanzu ba a dau ko guda daga cikinsu ba.

A wannan tsari na mayar da 'yan gudun hijira kasarsu, har ila yau gwamnatin Kamaru tare da sauran abokanta na hulda suka mayar da 'yan gudun hijirar Jamhuriyar Tsakiyar Afrika gida.

Sai dai kuma wasu daga cikin 'yan gudun hijirar sun ce lokaci bai yi ba na komawa kasarsu.

5- Ta fannin nishadantarwa kuma, bayan hukumar kwallon kafa ta Afrika ta janye wa Kamaru shirya gasar neman lashe kofin kwallon kafa na Afrika, ya rage mata wani babban kalubale na tabbatar da matsayinta na zakara wadda take rike da kofin.

Hakan dai ya sa bayan ta samu hayewa zuwa mataki na biyu na wasan, Kamaru ta kasa kwatar kanta a gaban 'yan wasan Najeriya, duk da cewa kuma tarin jama'a sun nuna mata kaunar da ta cilla har zuwa karshen wasa amma kuma hakan bai yiwu ba.