Yadda sauyin yanayi zai far wa Afirka

Fari na far wa wasu kasashen Airka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fari na far wa wasu kasashen Airka
An wallafa

Afirka na fuskantar sauyin yanayi fiye da ko'ina a duniya, cewar masanin dumamar yanayi Richard Washington.

Afirka ce nahiyar da dumamar yanayi za ta fi shafa.

Ga dalilai guda hudu nan:

  • Afirka na da alaka da yanayi sosai. Miliyoyin 'yan Afirka na dogara da lokacin damina domin su yi noma.
  • Tsarin lokutan yanayi a Afirka na da girma sosai. Za ta iya sauya wa sosai.
  • Yadda ake tsammanin sauyawar yanayin zai yi girma sosai. Zangon damina zai karu sosai a wasu sassan Afirka.
  • 'Yan Afirka ba sa iya sauya wa sauyin yanayi da ke aukuwa saboda fatara da talauci. Kazalika gwamnatoci ba su ba wa sauyin yanayi muhimmanci.

Sauyin Yanayi

Hamada da ke akwai a Afirka ta fi ko'ina yawa. Tana da kasa wadda tafi komai daukar zafi a duniya.

A watan Yuni da Yuli ana samun guguwa mai dauke da yashi wadda girmanta ya fi na ko'ina a duniya.

Wannan guguwa na shafar yanayi ta yadda har yanzu dan Adam bai fahimta ba a kimiyyance.

Wata mahaukaciyar guguwa mai dauke da kasa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wata mahaukaciyar guguwa mai dauke da kasa

Yankin ba ya da wasu duwatsu manya masu sauya yanayi, amma yana taimakawa wajen kawo ruwa na tsawon wata uku da ke yanke wata tara na rashin ruwa a tsakiyar yammacin Afirka da ke kudu daga Sahara.

Daga 1960 zuwa 1984, an samu ragowar yawan ruwan sama da kashi 30, a yammacin Afirka. Wannan ya yi sanadin fari inda dubunnan mutane suka rasa rayukansu, miliyoyi kuma suka rasa muhallansu.